1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro game da ɗumamar yanayi a ƙasar China

Sadissou YahouzaOctober 4, 2010

Ƙasashen duniya sun bayyana aniyar cimma yarjejeniya game da ɗumamar yanayi

https://p.dw.com/p/PUlh
Illolin ɗumamar yanayi kan tsaunukaHoto: dpa

Wakilai daga ƙasashe na duniya guda 170 ke halarta taro kan sauyin yanayi da ake gudanarwa a birnin Tianjin da ke a arewacin ƙasar China

Taron wanda ya biyo bayan taron Copenhague, shekara guda da ta wuce wanda kuma a kansa aka kasa cimma daidaituwar baki tsakanin ƙasashen kan rage yawan  hayaƙin  iskan gaz a duniya da ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na masana'antu ke fitarwa na zaman na ƙarshe wajan sammun haɗin kan ƙasashen akan manufofin rage ɗumamar yanayi kafin babban taron da aka shirya gudanarwa a cikin watan Disamba a birnin Cancun na ƙasar Mexiko

Da take magana da manema labarai babbar jam'iyyar Majalisar Ɗinkin ɗuniya kan al'amuran canji yanayi Christina Figueres ta yi gargaɗin cewa wannan ita ce ganawa ta ƙarshe kafin babban taron Cancun, saboda haka lokaci ya yi da za mu ƙoƙarin samun fahintar juna gabannin babban taron. 

Mawallafi: Abdourahman Hassane

Edita: Yahouza Sadissou Madobi