1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro kan yin amfani da kuɗaɗen shiga na harkokin ma'adinan nahiyar Afirka.

YAHAYA AHMEDNovember 9, 2006

Ko ta yaya ƙasashen nahiyar Afirka za su iya sa ido da kau da masu zamba a harkokin cinikayyar ma'adinansu? Ko ta yaya ne kuma za a ga cewa, an yi amfani da kuɗaɗen shiga da ake samowa daga cinikin ma'adin wajen inganta halin rayuwar jama'ar ƙasashen nahiyar? Wannan dai na cikin jigogin da wasu kungiyoyin sa kai suka yi tattaunawa a kansu.

https://p.dw.com/p/BtxT
Maiaktan haƙo lu'ulu'u a Saliyo.
Maiaktan haƙo lu'ulu'u a Saliyo.Hoto: picture-alliance/ dpa

Kyakyawar hanyar da za a iya bi wajen tabbatad da cewa, an kau da masu zamba a harkokin cinikayyar ma’adinan Afirka a kasuwannin duniya, ita ce bin misali ko kuma yin kwaikwayo da tsarin nan na Kemberly da aka ƙiƙiro don daidaita harkokin lu’ulu’u. Bisa wannan tsarin dai, duk masu harkar kasuwancin daimun, sai sun tabbatar cewa, yana da satifiket daga ƙasar da aka samo shi, kafin su yi cinikinsa. Wannan tsarin dai na da burin ganin cewa, an hana yin amfani da kuɗaɗen da aka samo daga ma’adinan wajen sayen makamai don ci gaba da yaƙe-yaƙen basasa, kamar a Angola, ko Laberiya, ko Saliyo. Abu Brima, na wata ƙungiyar sa kai daga ƙasar Saliyo, ya wakilci ƙungiyoyin sa kan ƙasarsa a gun taron tsai da shawara kan tsarin na Kimberly. A ganinsa dai, sharaɗin da aka gindaya, na bai wa duk daimun takardar shaida daga hukumar ƙasar da aka samo shi, na da fa’ida ƙwarai wajen bin diddigin yadda harkar lu’ulu’un ke tafiya a duniya. Sai dai, tsarin ba ya la’akari da ma’aikatan haƙo daimun ɗin, waɗanda har ila yau ke gudanad da aikinsu cikin mawuyacin hali:-

„Aikin haƙo ma’adinan dai aiki ne mai wuya. Binciken da muka gudanar na nuna cewa, an fi samun yawan talauci ma tsakanin ma’akatan haƙo daimun ɗin, fiye da sauran sassa da yankuna na ƙasarmu, inda babu ma’adinan. Duk waɗannan dai batutuwa ne da gwamnati ke sane da su, kuma suke cikin takardunta.“

Shi dai Brima, ya kara bayyana cewa, a matsugunan ma’aikatan haƙo daimun ɗin a Saliyo, babu ruwan sha mai tsabta, kuma babu kafofin kiwon lafiya ingantattu. Bugu da ƙari kuma, kamfanonin haƙo ma’adinan, sai ƙara ta da jama’a suke yi daga matsugunansu da filayensu.

Irin wannan halin dai, ba abu ne da ya kamata nahiyar Turai ta yi zaman oho ba ruwanmu tana kallo ba, inji Michael Hippler, babban jami’in kula da ɓangaren nahiyar Afirka, na ƙungiyar ba da agajin nan ta cocin katolika a Jamus, wato Misereor. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„A matsayinmu na masu amfani da waɗannan ma’adinan, mu ma muna da rawar takawa a wannan huskar. Idan dai yawan bukatun da muke yi wa ma’adinan ne ke sa ana haƙo su, to ashe kuwa wani babban nauyi ma ya rataya a wuyarmu.“

Su dai ƙungiyoyin sa kai na nan Jamus kamarsu Misereor, ko „Brot für die Welt“ ta cocin Evangelist na nan Jamus, ko kuma Medico International, suna ƙoƙartawa wajen ganin cewa an yi kula da inganta halin rayuwar ma’aikatan haƙo ma’adinan a matsugunansu. Ta hakan ne kuwa, za a iya yin amfani da wasu kuɗaɗen da ake samowa daga man fetur ko daimun wajen kyautata halin rayuwar talakawan yankunan da ake haƙo ma’adinan, inji Michael Hippler, na kungiyar Misereor:-

„A namu ganin dai, ana bukatar faɗakarwa ƙwarai da gaske. Sabili da haka ne, fafutukar bayyana wa al’ummomin da lamarin ya shafa hakkokinsu, ke da muhimmanci a matsayi na farko. Daga bisani kuma, kamata ya yi a bai wa ƙungiyoyin sa kan cikakken horo, don su iya tinkarar manyan kafofin gwamnati da na kamfanonin haƙo ma’adin don su iya nuna juriya wajen tatttaunawa da su, a matsayin wakilan jama’a talakawan.“

Akwai dai kyakyawan misali na aikin haɗin gwiwa, tsakanin ƙungiyoyin sa kai na yammacin Turai da kuma na nahiyar Afirka wajen cim ma wannan burin, a ƙasashen Cadi da Kamaru. A dangane da haƙo man fetur a Cadin dai, ƙungiyoyin kare muhalli da na hakkin bil’Adama, sun yi ta gwagwarmayar ganin cewa, an kula da halin rayuwar mazauna yankunan haƙo man. Wata lauya, Thérèse Mekombé, wadda ke wakilcin ƙungiyoyin mata a kwamitin sa ido kan yadda ake aiki da kuɗaɗen shiga na man fetur ɗin ƙasar Cadin, ta bayyana cewa, an cim ma gagarumin nasara a wannan huskar:-

„A yanzu dai an amince da mu tamkar abokan hulɗa. Idan muna da wani abin da za mu yi suka a kansa, to muna cikakken nazari ne tare da ba da misalai, waɗanda kuma muke bayyana su ga gwamnati ko kuma bankin duniya. To irin wannan fafutukar ne dai ta sa har aka ƙiƙiro kwamitin sa idon, inda ƙungiyoyin sa kai ke da wakilai huɗu a cikinsa. Wannan kwamitin dai na iyakacin koƙarinsa wajen bin diddigin duk kuɗaɗen shiga na harkokin man fetur ɗin, sa’anna kuma ya sanar da jama’a ko mene ne ma aka yi da kuɗinsu.“