1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro tsakanin Bush da Erdogan a fadar " White House "

November 5, 2007
https://p.dw.com/p/C14t

Nan gaba a yau ne, shugaban ƙasar Amurika Georges, Bush zai karɓi baƙuncin Praministan Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan.

Jim kaɗan kamin wannan ganawa, Erdogan ya hurta cewar haƙurin Turkiyya ya kai muƙura, a game da hare-haren yan awaren PKK.

Turkiyya ta zargi Amirika da kasa cewa oppan, a game da rikicin da ke wakana a iyakar Turkiya da Irak, inda yan awaren PKK ke ci karensu babu babbaka.

A ranar jum´a da ta wuce, sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta alƙawarta wa Turkiyya cewar, nan gaba,Amirika za ta ɗauki wannan matsala da hannu biyu, tare da tallafawa hukumomin ƙasar wajen fuskantar ƙalu balen yan awaren PKK.

A wata sanarwar da ta hiddo hjiya, gwamnatin Amurika, ta yi lale marhabin da belin sojojin Turkiyya da yan PKK su ka yi garkuwa da su.