1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro tsakanin Jamus da France a birnin Berlin

March 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5A

Yau ne, a fadar mulki ta gwamnatin tarayyar Jamus, a ka buɗa taron ministoci karo na 6, tsakanin ƙasashen Faransa da Jamus.

A na gudanar da wannan haɗuwa bisa jagorancin shugaban France, Jacques Chirak, da Angeler Merkell, wadda a karo na farko,ta ke hallartar taron, a matsayin shugabar gwammnatin Jamus.

Tawagogin ƙasashen 2, sun tantana batutuwan, da su ka shafi harakokin siyasa da diploamtia, hassali ma, batun wutar lantarki, da na baƙin haure, da ke ci ma ƙasashen turai tuwo a ƙwarya.

Kazalika, za su masanyar ra´ayoyi, a game da cutar murra tinstaye, da ke addabar France da Jamus.

Sannan, a dangane da batutuwan da su ka shafi siyasar dunia, magabatan 2, za su mahaura, a kan rikicin nukeyar ƙasar Iran, da kuma tura dakarun ƙungiyar gamayya turai, a Jamuhuriya Demokraɗiyar Congo.

A yayin da ta ke jawabi ga manema labarai, Angeller Merkell, ta bayyana amincewar, Faransa da Jamus na tura dakarun EU, a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, domin tabbatar da tsaro, albarkacin zaben da za a gudanar a watan juni mai zuwa.

To amma, hakan bai zai tabata ba, sai da izinin gwamnatin wannan ƙasa inji ta.