1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro tsakanin tawagogin India da na Pakistan

Yahouza S. MadobiFebruary 20, 2007

Hukumomin India da Pakistan sun alƙawarta haɗa ƙarfi domin samar da zaman lahia da kuma yaƙar yan ta´ada

https://p.dw.com/p/BtwA
Hoto: AP

A wani mataki na maida martani da hare-haren ta´adancin da su ka rutsa da jirgin ƙasar haɗin kai tsakanin India da Pakistan, hukumomin ƙasashen 2, sun jaddada aniyar su, ta ci gaba da tattanawa, a kann batun samar da zaman lahia, da kuma yaƙar yan ta´ada.

Idan dai za a iya tunawa, jiya ne wasu yan ƙunar baƙin wake su ka kai hari, ga jirgin ƙasar, da a ka raɗawa suna jirgin haɗin kan al´ummomin India da na Pakistan, wanda a sakamakon sa, mutane kussan 70 su ka rasa rayuka.

Jim kaɗan bayan kai harin hukumomin ƙasashen 2, su ka bayyana haɗa ƙarfi da ƙarfe, domin matsa ƙaimi wajen yaƙar yan ta´ada, da kuma ci gaba da tantanwa har sai sun cimma burin da su ka sa gaba, na samar da zaman lahia mai ɗorewa tsakanin ƙasashen, da su ka daɗe su na zaman ba ga maciji da juna.

A dangane da haka ne wata tawagar gwamnatin ƙasar Paskistan, bisa jagoranci ministan harakokin waje, Khurshid Kasuri ta kai ziyara yau a India.

A yayin da ta ke tsokaci a kan wannan al´amari kakakin gwamnatin India,ta ce wanda su ka kai wannan hari, wajen ruwa sun samo iska, ta la´akari da ƙara fahintar juna da a ka samu, tsakanin gwamnatocin India da Pakistan.

Bayan ganawar da aza ayi yau, tsakanin tawagogin 2, ita ma hukumar mussamman da su ka girka, tun shekara ta 2004, za ta shirya na taro gobe laraba da zumar ƙara cimma daidaito a kan matsalolin da ke raba kawunan al´umomin India da Pakistan.