1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasa da ƙasa a game da harakokin sadarwa na gudana a Doha

March 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5c

A birni Doha na kasar Qatar,an fara taron ƙasa da ƙasa, a game da matakan rage giɓin hanyoyin sadarwa tsakanin ƙasashe masu arzikin masana´antu da masu fama da talauci.

A tsawan sati ɗaya, mahalarta wannan babban taro, su fiye da dubu ɗaya, za su mansayanr ra´ayoyi, a kan mattakan ƙara ƙarfafa hanyoyin sadarwa na zamani, a ƙasashe masu tasowa, inda fiye da mutane million dubu, bas u da damar mallakar sallula, kokuma shiga Internet, sanɓanin ƙasashe masu ci gaban masana´antu, inda wannan kafofin sadarwa su ka zama ruwan dare.

Wasu alƙalluma, da ƙurraru ta fannin sadarwa su ka gudanar, sun bayyana cewar, a shekara ta 2004, nahiyar Afrika, ta ƙunshi kashi 13 bisa 100, na al´ummomin dunia, saidai ƙasa ga kashi 4 bisa 100, na jama´ar ta, ke da wayoyin tafi da gidan ka, kokuma na girke.