1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashe masu ƙarfin tattalin ariki a duniya

June 27, 2010

'Yan sanda sun ƙara capke masu zanga zanga a wajan taron ƙasashe masu arzikin masana'antu da ake yi a birnin Toronto

https://p.dw.com/p/O4Yn
Masu zanga zangar nuna adawa da Taro G20Hoto: AP

Shugabannin ƙasashen duniya guda 20 masu ƙarfin tattalin arzikin masana´antu dake gudanar da taro a birnin Toronto na ƙasar kanada,sun ɗauki alƙawarin rage giɓin da ake samu na kuɗi a ƙasahensu domin ƙara inganta al'amuran tattalin arziki.Shugabannin dukaninsu masu ƙoƙarin neman cigaba ,a ƙarshen sun samu fahimtar juna wajen rage yawan kuɗaɗen basusukan ta yadda kowace ƙasar zata yi nata tsarin.Shugaban ƙasar Kanada wanda shine ke da masaukin baƙin ya yi fatan ganin an ɗauki alƙawarin rage da kashi ɗaya bisa biyu, kafin nan da shekara ta 2013.

Sanan kuma da rage yawan kuɗaɗen bashi,wanda a ƙarshe wannan alƙaura aka saka su a cikin sanarwa ƙarshe da taron na G20 zai bayyana.Ana dai cikin gudanar da taron shugabannin ƙasashen Jamus da Ingila suka fuce daga zauren taron domin kallon wassannin cin kofin duniya na ƙwallon ƙafa wanda a kansa Jamus ta lashe Ingila da ci Huɗu da ɗaya .

Yanzu haka kuma hukumar ´yan sanda a ƙasar ta Kanada ta bada sanarwa ƙara capke wasu jama´ar dake zanga- zangar nuna adawa da manufofin ƙasashen duniyar masu ci-gaban masana´antu.

Wani kakakin ´yan sandar, Saja Tim Burrows ya shaida cewa ya zuwa yanzu sun kame mutane 584 bayan ƙwone ƙwone da aka yi tun can da farko wanda aka ɗora alhakinsu akan wata ƙungiya ta masu fafutukar kare muhhali .

Mawallafi :Abdourahamane Hassane.

Edita : Yahouza sadissou Madobi