1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

250909 G20 Auftakt

Zainab MohammedSeptember 25, 2009

Yini uku kafin zaɓen Jamus, Angela Merkel ta nanata matsayinta kan tabbatar da sauyi a kasuwannin hada-hada

https://p.dw.com/p/Joft
Hoto: AP

Ƙungiyar ƙasashe masu cigaban masana'antu na G-20, ta amince da zama wadda zata lura da batutuwan da suka jiɓanci tattalin arziki na Duniya, wanda keda alaka da sabbin matakai kan tattali, inda ƙasashe kamar Sin zasu yi tasiri.

Shugabannin ƙasashen G20 masu cigaban tattalin tattalin arziki, sun kuma amince da cewar hukumar bada lamuni ta Majalisar Ɗunkin Duniya ta IMF, ta samu ƙarin wakilci. Ta hanyar kara yawan ƙasashen da zasu iya jefa kuri'u, musamman a ɓangaren waɗanda a baya basu da wakilici, ko kuma keda ƙalilan.

Haka dai na nufin sauya matsayin hukumar na yanzu daga kashi 57 daga cikin 100 a ɓangaren ƙasashe masu cigaban masana'antu, kana 43 a ɓangaren masu tasowa, zuwa a kalla 'yanci daidai, ma'ana 50 da 50 kenan daga cikin 100.

A shekara ta 1999 nedai aka kafa ƙungiyar ta G20 wa ministocin harkokin kuɗi da shugabannin Manyan Bankuna, sakamakon rikicin tattalin da yankin Asia ya shiga. Maƙasudun hakan dai shine taimakawa ƙasashe masu karfin tattalin arziki na G7, da suka haɗa da Amurka, Jamus, Britaniya, Faransa, Japan, Italiya da Canada, yanayin da zasu yi hulɗa da Duniya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ke halartan taron na Pittsburgh da ministan harkokin kuɗin ƙasar Peer Steinbrück, ta bayyana matsayin Jamus dangane da wannan taron.

Bundeskanzlerin Angela Merkel bei Regierungserklärung zu Afghanistan
Angela MerkelHoto: picture alliance/dpa

Tace a Pittsburgh ya zamanto wajibi a zartar da matsayi, dangane ko batun dokokin kawo sauyi a harkokin kasuwannin hada-hadan kuɗi zai cigaba da samun fifiko. A na mu ɓangare wannan shine, babban abunda yake da muhimmanci. A nazarin na a yanzu muna kan hanya madaidaiciya, amma zai iya samun rauni, idan akwai sauyin alkibla. Dangane da haka ne daga ɓangarenmu zamu yi iya kokarin ganin cewar hakan bata kasance ba. A kan hakan ne nace wannan zai kasance batu mai sarkakkiyya, dangane da cewar ko batun dokokin kasuwannin hada-hadar kuɗaɗe zasu cigaba da zama abunda zamu mayar da hankali akai.

A bayyane dai shugabar gwamnatin Jamus ɗin na ganin cewar Amurka da Britania zasu karkata. Gabannin taron dai shugaban Amurka ya gabatar da sabbin batutuwan rashin daidaito a harkokin kasuwanci, waɗanda ya nemi ayi muhawara akansu a taron. Shin waɗanne irin matakai suka cancanta a ɗauka? ko kuma kamata yayi kowace ƙasa ta tsara manufofin da zata cimma da kanta a kowace shekara?

Bundesfinanzminister Peer Steinbrueck
Peer SteinbrückHoto: AP

Ministan harkokin kuɗi na tarayyar Jamus Peer Steinbrück, yace baya adawa da wannan batu sai dai yace, da zanyi matukar farin ciki, idan da an gabatar da wannan batu na rashin daidaito a gaban ministocin harkokin kuɗi. Domin wannan batu ne dake da matukar muhimmanci a rikicin kasuwannin hada-hada da ake ci. Amma batu na gaskiya shine, bari muyi magana dangane da giɓin kasafin kuɗin Amurka, da kuma irin ɗumbin kudaden da yanzu suka kasance wajibi su shiga Amurka domin rufe wannan giɓin. Kuma wata matsala iatace da har yanzu ba za a iya canja kuɗin Sin ba. Don haka babu wani dalilin da zai sa a mahance wannan matsala, amma kada ayi zaɓi, a dubi batun ba ɗaya.

A yanzu haka dai ƙungiyar ta G20 ta tsayar da cewar, a matsayinta na jagorar halin tattalin arzikin da Duniya take ci, hakki ya rataya a wuyanta na cigaba ta ayyukan haɗaka , koda kuwa an farfado daga yanayi na yanzu.

To ganin irin gagarumin matsayi ta ƙungiyar ta ɗora kanta, ko hakan na nufin rusa ƙungiyar G8 masu karfin tattalin arziki kenan a fakaice?