1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen ƙungiyar IGAD a Nairobi

June 13, 2006
https://p.dw.com/p/Buu9

r.

Ƙasashe 7, na yankin gabancin Afrika,membobin Ƙungiyar Igad, sun ƙaddamar da zaman taro yau, a birbin Nairobi na ƙasar Kenya.

Ministocin ƙasahen na tantanawa, a game da halin da a ke ciki a ƙasar Somalia.

Su na masu tunanin tura tawagar kwantar da tarzoma, ta haɗin gwiwa, to saidai dakarun kotunan musulunci, da ke riƙe da Mogadiscio a halin yanzu, sun yi wasti da wannan mataki.

A ɗaya hannun kuma, mahalarta taron Nairobi, sun bayyana buƙatar saka takunkumi, ga shugabanin dakarun haɗin gwiwa na Somalia da ke samun goyan baya daga Amurika, domin kiffar da kotunan musulunci.

Tunni, hukumomin Kenya, sun haramtawa wannan shugabanin shiga ƙasar.

A nasa ɓangare, komishinan bada agaji, na ƙungiyar gamayya turai, wanda a halin yanzu, alolin Somalia, ranar alhamis mai zuwa a birnin New York. ke ƙasar Kenya, ya bayyana aniyar EU, ta tallafawa hallatattun hukumomin Somalia.

Sannan ƙasar Amurika, ta fito hili, ta bayyana cewar, haɗin gwiwar da ta baiwa dakarun sa kann Somnalia bai cimma nasara ba,a game haka, ta girka komiti na mussamman wanda zai tantana matsalar Somalia