1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen Afrika a game da citar Sida a birnin Brazaville

March 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5e

A birnin Brazaville na Jamhuriya Afrika ta tsakiya, wakilai daga kasashe Afrika, tare da ƙurrarun ta fannin kiwon lahia, na ci gaba da zaman taro, a game da batun cutar Aids, ko Sida a nahiyar Afrika.

Hukumar Majalisar ɗinkin Dunia mai yaki da Aids ta gayyaci wannan taro na kwanaki 3.

Jawabai daban daban da a ka gudanar, sun bayyana rashin samun nasarar murƙushe wannan cuta.

Duk da magudan kuɗaɗen da Majalisar Ɗinkin Dunia, da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ke sakawa a yaƙin, abun,ya zama tamkar a na magani kai na ƙaba, ta la´akari da yaɗuwar cutar kamar wutar daji.

Shugaban hukumar yaƙi da Sida, a Majalisar Ɗinkin Dunia Michel Sidibe,ya ce duk shekara ta Allah,a na samun ƙarin mutane million 3, a nahiyar Afrika, da ke kamuwa da cutar Aids, sannan tan a hallaka mutane kussan million 3 a ko wace shekara, a nahiyar Afrika, tare da barin marayu million 14 cikin.

Mahalarta wannan taro, sun shawarci sake shiri, da sake sallon yaƙi da cutar Sida a Afrika.