1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙoli tsakanin Russia da Jamus

October 14, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8Z

Nan gaba a yau ne a birnin Wiesbaden dake nan Jamus, shugabar gwamnati Angeller Merkel,zata gana da shugaban ƙasar Russia Vladmir Poutine, a game da rikicin yankin Kosovo.

Bayan rikicin na Kosovo,tawagogin ƙasashen 2, za su tantana a tsawan yini 2, a game da sauran batutuwa da su ka shafi mu´amila tsakanin su, da kuma harakokin diplomatia na dunia, mussaman rikicin nuklear ƙasar Iran.

A yayin da ta ke bayyani a jajibirin buɗe taron, Angeller Merkel, ta kyautata zaton ciwo kann shugaba Poutine, a game da wajibcin daina bada goyan baya ido rufe, ga hukumominTeheran a dangane da taƙƙadamar nuklea.

A ɗaya ɓangaren, magabatan za su masanyar ra´ayoyi a game da mu´amilar kasuwancin tsakanin su.

A farkon wattani 6 na shekara da mu ke ciki, saye da sayarwa tsakanin Jamus da Russia, ya ƙaru da kashi 13 cikin ɗari idan a ka kwantanta da shekara da ta gabata.