1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Ƙungiyar APEC a Hanoi.

November 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bubt

Ƙasashe 21, membobin ƙungiyar cinikaya a yankunan Asia, da Pacific, na ci gaba, da zaman taro a birnin Hanoi na ƙasar Vietnam.

Sakatariyar harakokin wajenAmuruika Condoleesa Rice, na daga mahalarta wannan taron tattalin arziki.

A jawabin da ta gabatar Rice, ta maida hankali a kan batun yaƙi da ta´danci da kuma yaɗuwar ƙananan makamai, wanda ke kawo cikas, ga al´ammuran faɗaɗa saye da sayarwa, a dunia.

Condoleesa Rice, ta gayaci ƙasashen ,sun maida himma ,wajen yaƙar wannanmatsaloli.

Za a kai ƙoluluwar taron na Apec, ranar assabar mai zuwa, tare da halartar shugabanin ƙasashen Russia, China da Amurika.