1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyar Cen-sad a Tripoli

June 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buvj

Yau ne a birninTripolie na ƙasar Lybia, a ka buɗa taron ƙungiyar CEN-SAD, da ta ƙunshi ƙasashe 23, na Afrika, dake yankunan Sahel da Sahara.

Shugabanin ƙasashe 11, da su ka haɗa da Hosni Moubarack na Masar, da Omar El Bashir na Sudan, da Blaise Kampaore, na Burkina Faso, su ka halarci wannan taro, da shugaba Muhhamar kahdafi ke jagoranta.

A jawabin sa na buɗe taron , shugaba mai masaukin baki, yayi kira da babbar murya, ga ƙasashen Sudan da Tchad, da su ɗinke ɓarakar da ke tsakanin su.

A ɗaya wajen, ya bayana takaici, a game,da tsaida tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor, wanda a cewar sa, ya nuna jarumtaka, ta hanyar sauka daga muƙami, salin alin, don kwanciyar hankali ta dawo a ƙasar Liberia.

Miƙa Charles Taylor, ga kotun ƙasa da ƙasa, ya zama abun kunya, ga hukumomin Nigeria, da ma Afrika baki ɗaya, a cewar Ƙhaddafi.

Mahimman batutuwa da shugabanin ke tantanawa kansu a tsawan yini 2,sun haɗa da rikicin yankin Darfur, bayan yarjejeniyar da aka cimma a birninAbuja na taraya Nigeria.

Kazalika za su duba halin da ake ciki a ƙasar Somalia da Cote d´Ivoire.