1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyar NATO a game da rikicin yankin Darfur

April 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv26

Wakilan kasashe 26, membobin Ƙungiyar tsaro ta NATO kokuma OTAN,sun fara zaman taro yau laraba, domin tantana batun tallafin ƙungiyar ga harakokin tsaro a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Ƙungiyar tsaro ta Nato, ta samu goran gayyata, daga Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, Koffi Annan, na aika gudumuwa sojoji, da kayan aiki, domin tallafawa dakarun shiga tsakani na ƙungiyar taraya Afrika, su 7.000 da ke yankin Darfur.

Sakatare jannar na NATO,kokuma OTAN, Jaap de Hoop Scheffer, ya buƙaci ƙungiyar ta yanke shawara cikin gaggawa, ta la´akari da matsanancin hali da al´umomin Darfur ke fuskanta.

Saidai sakataran ce, a halin da ake ciki, babu batun tura dakarun NATO, a wannan yanki, kasancewar adawa, da hukumomin Sudan ke yi, da matakin.

Babban tallafin da NATO kan iya badawa, ba zai wuce ƙara ƙarfin gwiwa ba, ta fannin kuɗaɗe, da kayan aiki, da kuma ƙurrarun massana, a kan harakokin yaƙi, ga rundunar tsaron Afrika.