1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyar SADC a Dar es Salam

March 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuOw

Idan an jima kaɗan ne, ƙasashen yankin Kudancin Afrika na ƙungiyar SADC, za su buɗa zaman taro a birin Dar-es Salam na ƙasar tanzania.

Ƙasashe 14 membobin wannan ƙungiya sun sha suka daga ƙasashen dunia, a game da halayen ko in kulla da su ka nuna, a kan uƙubar da gwamnatin Robert Mugabe na Zimbabwe, ke ganawa yan adawa.

A tsawan kwanaki 2, shugabanin ƙasashen SADC, za su cenza miyau, a kan mattakan bai ɗaya na warware rikkicin siyasar Zimbabwe.

Kazalika, za su anfani da wannan dama, domin tantana batun rikicin Jamhuriya Demokradiyar Kongo, inda a cewar jikadan Jamus a birnin Kinshasa, mutane 200, zuwa 500, su ka rasa rayuka, tsakanin 22 zuwa 23 ga watan da mu ke ciki ,a yayin arangama da ta haɗa dakarun madugun yan adawa, Jean Piere Bemba da rundunar Gwamnati.