1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Ƙungiyar Tarayyar Turai da China

October 6, 2010

Ƙungiyar Tarayar Turai da China sun fara wani taro a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam.

https://p.dw.com/p/PXTf
Tutocin Ƙungiyar Tarayyar Turai da China.Hoto: AP

A birnin Brussels ana nan ana gudanar da taron tsakanin Ƙungiyar Tarayyar Turai da China inda ake sa ran shiga takun tsaƙa game da darajar kuɗin China. Amirka da China dai na zargin juna ne da rage darajar kuɗinsu domin haɓaka cinikin da suke yi da ƙasashen ƙetare da kuma bunƙasa tattalin arziƙinsu. Gwamnatin Amirka ta ce za ta ɗauki mataki mai tsauri akan kuɗin Yuan da China ke amfani da shi. A saboda haka ne ma majalisar wakilan Amirka ta ƙaƙaba kuɗin fito akan hajojin China. A dai halin da ake ciki yanzu Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi kira ga China da ta kara darajar kuɗinta domin ba ƙasashenta damar shiga kasuwannin duniya. Bisa ga dukkan alamu babban bankin Tarayyar Turai zai ƙara kuɗin ruwan da yake karɓa domin ta da komaɗar kuɗin Euro da kuma ƙara farashin hajojin da ƙasahenta ke shiga da su kasuwannin ƙetare.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal