1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa a birnin Berlin a game da Global Fond

September 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuA7

Wattani 3 bayan taron ƙasashen ƙungiyar G8, a Heilgendam na Jamus, ƙasar ta sake karɓar wani babban taro na ƙasashe masu hannu da shuni, da ƙungiyoin bada tallafi.

Taron na birnin Berlin, da za a kammalla nan gaba a yau, na gudanar da mahaurori, a game da hanyoyin samar da kuɗaɗen cikka assusun taimako na ƙasa da ƙasa, mai suna Glabal Fonds, wanda ke bada kuɗin da ake anfani da su, wajen yaƙi da manyan cututuka guda 3 wato Sida, tarin fuka, da massasara cizon sabro, wanda su ka fi hadasa mace mace, mussamman a nahiyar Afrika.

Wanda su ka shirya wannan taro, na kyauttata zaton tattara ƙarin kuɗin da yawan su zai kai dalla milion 8 a ko wace shekara,tsakanin shekara ta 2008 zuwa shekara ta 2010, a cikin wananan assusu,wanda tsofan sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, ya ƙirƙiro a shekara ta 2002.

A cewar shugaban hukumar yaƙi da cutar Sida na Majalisar Dinkin Dunia, Peter Piot ,a halin yanzu ƙasashen da ƙungiyoyin da ke halartar wannan taro, sun alkawarta taimakawa da jimlar kudi dalla milion dubu 10, tsakanin shekara ta 2008 zuwa 2010 a cikin wannan sasusu.