1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron addinan duniya a garin Assisi.

YAHAYA AHMEDSeptember 7, 2006

Shugabannin addinan duniya da dama ne suka halarci wani taron Ibada a garin Assisi na ƙasar Italiya, a bukuwan cika shekaru 20 da gudanad da wannan taron a karo na farko. A cikin shekarar 1986 ne dai tsohon Papa roma John Paul na II, ya kira wannan taron, indda shugabannin addinan duniya suka taru don su yi addu'ar samad da zaman lafiya a duniya.

https://p.dw.com/p/BvTK
Marigayi Papa roma John Paul na II, lokacin taron Assisi a 1986.
Marigayi Papa roma John Paul na II, lokacin taron Assisi a 1986.Hoto: AP

Tun shekaru 20 da suka wuce ne tsohon Papa Roma, marigayi Johannes Paulus na biyu, ya gayyaci shugabannin manyan addinan duniya zuwa garin Assisi don halartar wani taron addu’o’i da ibada mai burin cim ma zaman lafiya a duniya. Mabiya addinan Bhudha, da Hindu, da Islama da Yahudu da duk wasu muhimman ɗariƙun kirista ne suka amsa wannan kiran.

A wannan shekarar kuma, ɗariƙar nan Sant Egidio ta cocin Katolika, wadda tun da ma can take shirya irin waɗannan tarukan, ta gayyaci mabiya addinan duniyar zuwa Assisi. Shugaban ɗariƙar cocin orthodox na Siriya Mar Gregorius, wanda shi ma ya kasance a Assisin, ya bayyana ra’ayinsa game da taron ne kamar haka:-

„Lokacin da muka fara zuwa nann Assisi, ba a tsai da shawarar ci gaba da wannan taron ba. Da yawa daga cikinmu dai ba su yi zaton cewa, za a ci gaba da gudanad da taron ba. Amma daga baya, sai kowa ma ya gane muhimmancin wannan taron, da yadda ya shimfiɗa wata gadar zumunci tsakkanin shugabannin addinan duniya. Da can a ƙasarmu, ba a iya ganin wannan cuɗanyar ta zumunci. Amma tun farkon taron da aka yi a Assisi, shugabannin Islama da na Kirista a ƙasata Siriya na ci gaba da tuntuɓar juna.“

Babu shakka, tarukan ibadan da aka yi ta yi tun 1986, sun janyo sassaucin tsamari tsakanin Duniyar Musulmi da kasashen Yamma. Ta hakan ne ma, aka cim ma wata yarjejeniya tsakanin jami’ar Al-Azhar ta birnin al-ƙahira da Vatican, don gudanad da tarukan haɗin gwiwa kai da kai. Shugaban jami’ar ta Al-Azhar, Ahmed al Tayyeb, shi ma ya halarci taron ibadan na Assisi a wannan shekarar, inda a cikin jawabinsa, ya bayyana cewa:-

„Na kawo muku saƙo, ku ’yan Sant Egidio, musamman daga Al-Azhar, saboda ƙwazo da hakurin da kuke nunawa a kan wannan hanyar ta samad da zaman lafiya. Duk waɗanda ke aiki da kuma addu’a don samad da zaman lafiya, da musulmi da waɗanda ba musulmi ba, na jinjina muku a wannan ranar ta cika shekaru 20 da farkon taron da aka yi, kuma suna yi muku fatan alheri a duk yunƙurin da kuke yi na samad da zaman lafiya.“

Yayin da a da can harkokin siyasa da na tattalin arziki ne suka fi jan hankullan mafi yawan addinan, a yanzu shugabannin addinai da dama a duk duniya baki ɗaya, sun duƙufa ne wajen komawa ga tushensu na wanzad da zaman lafiya tsakanin al’ummomi. Kamar yadda wani shugaban ɗariƙar Tendai ta addinin Budha na Japan, Gijun Sugitani, ya bayyanar:-

„A lokacin da na fara zuwa nan Assisi, a shekaru 20 da suka wuce, zan iya tunawa da fara’ar da na yi yayin da muka taru muna addu’a. Kowa ya amince da ɗan’uwansa. Yanzu dai a ko’ina, addinan duniya sun fara aikin haɗin gwiwa don neman zaman lafiya. Ba a gunmu a Japan kawai ba, har kuma da Mozabique, da Saliyo, da Bosniya, da Sri Lanka da wurare da dama na duniya. Na tabbatar cewa, wannan manufar da muka sanya a gaba a nan garin Assisi, za ta yaɗu zuwa duk duniya, ta yadda addinan da muke bi, za su zamo wata hanya ta samad da zaman lafiya.“