1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Afrika da India a New Delhi

Yusuf IdrisApril 7, 2008

Shirin taron haɗin gwiwa tsakanin India da ƙasashen Afrika 15

https://p.dw.com/p/Ddtn
Kasuwar Mangoro a India.Hoto: AP

India da Ƙasashen Afrika zasu ƙaddamar da wani shiri da zai ɗaukaka Dangantaka dake tsakanin su,a wani taron yini biyu na farkon irinsa da India ta ɗauki nauyi a birnin New Delhi a wannan mako da zai haɗar da ƙasashen Afrika goma sha huɗu.

Taron zai taimaka wajen kyautata wannan dangantaka kuma zai buɗe wasu hanyoyin haɗin kai tsakanin ɓangarorin biyu.

Fiye da shekara ɗaya bayan ƙasar China ta gudanar da taron ta na ƙasashen Afrika inda ta tattauna harkokin kasuwanci a birnin Beijing,ita ma ƙasar India zata gudanar da nata taron da ƙasashen na Africa a wani yunƙuri na bunƙasa kasuwanci da cinikayya a nahiyar.

Taron ɓangarorin biyu dai,wanda ake sa ran a kalla shugabannin ƙasashen Afrika goma sha biyar zasu halarta,zai gudana ne a birnin New Delhi a wannan mako.Gabannin taron, manyan Jami'an gwamnati da Wakilan kafafen yaɗa labarai da ministocin harkokin waje ƙasashen waje zasu gudanar da tarurruka na sharan fage.

Wani Babban ɗan jarida na Najeriya Tunde Rahman ya ce taron yana da muhimmancin gaske,

"yana da muhimmanci,idan aka yi la'akari dashi,duk dacewar bazan so fadi ba,amma wannan shine karo na farko da shugabannin ƙasar India da na Afrika zasu haɗu a wuri ɗaya.zTaron zai tattauna abubuwa masu muhimmanci da zasu karfafa haɗin kai tsakanin nahiyoyin biyu.Ina tunanin yana da muhimmancin gaske saboda India da Afrika nada tarihi iri ɗaya na gwagwarmayar adawa da mulkin mallaka."

Kasuwanci tsakanin India da Afrika na bunƙasa sosai a cikin shekarun baya bayan nan,kuma za a iya gwada hakan saboda kasuwanci tsakanin ɓangarori biyu,ya ruɓanya tsakanin shekara ta dubu biyu da daya zuwa ta dubu biyu da shida, daga dalar amurka miliyan shida, zuwa kusan dala miliyan goma sha biyu.Kiyasin baya bayan nan ya nuna cewar kasuwancin ya ɗara dala biliyon goma sha biyu da da kaɗan.

Taron,wanda zai share fagen wani babban taron da zai kunshi dukkan ƙasashen afrika 54 nan da 'yan shekaru masu zuwa,zai nemi hanyar shimfiɗa matakai na samun nasara akan harkokin tattalin arziki da cuɗanya.Morgan Chonya na ƙasar Zambia,ya ce taron zai samar da hanyar inganta tattalin arziki,

"Na ga kyakkyawar hanya nan gaba saboda ƙasar India ta riga ta zuba jarin kuɗaɗe masu ɗimbin yawa a nahiyar,wannan kuma zai ba ƙasashen biyu damar cimma wata yarjejeniya da zuba jari da kuma ba wakilai daga India damar saduwa da abokansu daga wasu ƙasashen,don samar da yanayi na samun dangantaka akan harkokin zuba jari."

Tattaunawar dai zata fi maida hankali ne akan harkokin cinikayya,zuba jari,makamashi,demokraɗiyya,gyare-gyaren Majalisar Ɗunkin Duniya,zaman lafiya da tsaro da kuma ta'addanci.

Duk da cewa ƙasar India da nahiyar afrika sun daɗe suna tattaunawa a waɗannan bangarorin,wannan taron zai sa tattaunawar ta zama mafi ma'ana ta kuma ƙarfafa haɗin gwiwa.

Rahman ya ci gaba da cewa,

"ƙasar India da afrika na da kashi ɗaya daga kashi uku na yawan jama'a a duniya.Da irin wannan yawan jama'a,zata iya yin tasiri.kuma afrika zata iya cin moriyar Fasahar ƙasar ta India.Kasancewar mu tare daga nahiyoyin biyu haka,akwai abubuwa da dama da zamu iya yi"

An jima ana nazarin wannan taro na haɗin gwiwa tsakanin India da Afrika,sai dai ana jiran lokaci na tabbatar da hakan,wanda za a iya cewa yanzu ya zo.