1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Afurka da Turai

Ahmad Tijani LawalDecember 7, 2007

Taimakon raya Kasashen Afrika

https://p.dw.com/p/CYt8
Shugaba Robert Mugabe na ZimbabweHoto: AP

Afrika/EU

Babban abin da ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon shi ne taron kolin shuagabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Afurka da na kasashen Kungiyar Tarayyar Turai a Lisbon, fadar mulkin Portugal. Wannan taron zai fi mayar da hankali ne akan matsalolin Afurka da kuma dangantakar kasashen Afurka da na Turai. Jaridar Süddeutsche Zeitung tayi amfani da wannan dama don gabatar da wata budaddiyar wasika da wasu gaggan jami’ai da suka hada da ‚yan siyasa da mawallafa na Afurka da na Turai suka gabatar inda suke sokar dangantakun sassan biyu: Jaridar sai ta kara da cewar:

„Zai zama babban kuskure idan taron kolin EU da AU ya kasa yin amfani da wannan dama domin duba wasu gaggan matsaloli na jinkai guda biyu dake addabar Afurka yanzu haka. Wadannan matsalolin sun hada ne da halin da ake ciki a Darfur da Zimbabwe. Duk da cewar wajibi ne akan kasashen na Turai da Afurka su ba da la’akari da wannan batu, amma ba a shugar da shi a ajendar taron ba, walau a hukumance ko ba a hukumance ba.“

Afrika-EU

A zauren taron kolin dai kamar yadda aka ji daga shelkwatar Kungiyar tarayyar turai dake Brussels, shuagabannin kasashen Kungiyar ba zasu yi wata-wata ba wajen tinkarar shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe da korafi a game da take hakkin dan-Adam a kasarsa. Bayan da tayi wannan bayanin jaridar kasuwanci ta Handelsblatt cewa tayi:

„Duk da cewar taron zai yi bitar dangantakar kasuwanci tsakanin sassan biyu, amma fa kawo yanzun babu wata daidaituwar da aka cimma a game da bude kofofin kasuwanninsu bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi akan wannan batu. A makonni biyu da suka wuce wasu kasashe hudu na kudanci da kuma wasu biyar na gabacin Afurka sun cimma yarjejeniyar sassauta cinikin hajoji tsakaninsu, amma gaggan kasashe masu kakkarfan tattalin arziki da suka hada da ATK da Namibiya sun ki su shiga karkashin inuwar wannan yarjejeniya.“

Kawo yanzun dai manufofin taimakon raya kasa ba su taimaka kwalliya ta biya kudin sabulu a game da raya makomar nahiyar Afurka ba. A wani rahoton da ta bayar jaridar Internationale Politik dake nazarin dangantakar kasa da kasa ta saka ayar tambaya a game da dalilin wannan gazawa da kuma ire-iren darussan da za a iya koya daga gare ta. Jaridar ta ci gaba da cewar:

„Tun bayan gabatar da manufar taimakon raya kasashe masu tasowa a daidai lokacin da kasashe matasa suka fara samun ‚yancin kansu daga ‚yan mulkin mallaka a cikin shekarun 1950 an kashe dubban miliyoyin dala, amma fa har yau babu inda aka kai. Wasu daga cikin kasashen ma sun shiga matsaloli ne da suka gwammace jiya da yau. Daya daga cikin ummal’aba’isin wannan rashin nasara shi ne kasancewar an gabatar da manufar ne akan turbar yakin cacar baka tsakanin kasashen gabaci da na yammacin Turai, inda kowane bangare daga cikinsu ke fafutukar yada angizonsa.“

Taimakon Raya Kasa

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi bitar rashin fa’idar manufofin taimakon raya kasa, kamar yadda aka gani a cikin shekaru 50 din da suka wuce. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

„Duk wanda yayi nazarin mawuyacin halin da mutane ke ciki a nahiyar Afurka zai ga cewar taimakon raya kasar bai tsinana musu kome ba. Kimanin kudi dalar Amurka miliyan dubu 600 na taimako suka kwarara zuwa kasashen Afurka, amma hakan bai taimaka aka samu kyautatuwar rayuwarsu ba. Ikirarin da bankin duniya ke yi na samun raguwar yawan matalauta ‚yan rabbana ka wadata mu a duniya daga kashi 29 zuwa kashi 18% ya danganci kasashen China ne da Indiya, wadanda yawan taimakon da suka saba samu bai zarce kashi 0.5% na jumullar abin da suke samarwa a shekara ba.“