1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron AIDS a Berlin

Yahouza S.MadobiOctober 11, 2006

Wakilai daga Ƙasashe daban-daban na dunia na ci gaba da mahaura a game da cutar AIDS a birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/Btxm
Hoto: AP

Shekaru 25 bayan gano cutar ƙanjamau a dunia, har yanzu wannan mumunar annoba, na matsayin barazana ga rayuwar ƙananan yara, mussamman a ƙasashen yankin kudancin Afrika.

A birnin Berlin nan ƙasar Jamus an gudanar da taro a game da cutar inda wakilai daga sassa daban-daban na dunia, su ka yi bitar halin da ake ciki a dangane da cutar Sida

Alƙalluma sun nunar da cewa, kimanin rabi, daga mutanen da su ka kamu da cutar Aids ko kuma Sida, matasa ne yan ƙasa ga shekaru 25 da aihuwa.

Sannan a faɗin dunia baki ɗaya, akwai marayu sanadiyar cutar, a ƙalla milion 15 da ke fuskantar ƙyama da wariya cikin jama´a.

A faɗin dunia gaba ɗaya ƙananan yara million 2 ,da dubu ɗari 3 su ka tsinci kan su a cikin uƙubar cutar ƙanjamau, kashi bisa 100 na yawan yara da ke kamuwa da cutar na ƙasa da shekaru 15 a dunia, sannan kashi 87 bisa 100 daga cikin su, sun kasance a yankin kudancin Afrika.

Saidai idan aka ɗauki jimilar yawan kamuwa da cutar, ƙasar India ke sahun gaba a dunia.

Albarkacin taron da ya wakana a birnin Berlin na ƙasar Jamus hukumar Majalisar Dinkin Dunia, mai kula da ƙananan yara, wato UNicef,ta ja hankalin mahalarta taro a game da wannan,matsala, wadda ciwo kanta, ke buƙatar ƙarin tallafin kuɗaɗe, da kuma ƙarin kulla daga magabata.

A cewar Heide Simonis shugabar hukumar Unicef a nan ƙasar Jamus, ƙanana yara masu fama da cutar Aids basu samun kullawar da ta dace, domin a cewar ta:

A shekaru 2 da su ka gabata, a cikin ko minti ɗaya, yaro ɗaya ke kwanta dama, sanadiyar cutar Sida, ya zuwa yanzu, fiye da yara marayu million 15, iyayen su su ka mutu, dalili da wannan cuta.

Wakilin mussaman na MDD a game AIDS a nahiyar Afrika, Stephen Lewis ya gatar da jawabi a wannan babban taro, inda ya yi bayyani a game da ƙaranci kuɗaɗe da kuma baban haɗarin da wanda ke ɗauke da cutar ke ciki a wannan nahiya:

„Kashi 5 zuwa 10 bisa 100 ne kaɗai na yaran da su ka kamu da Sida a Afrika, ke samun maganin rage raɗaɗin cutar, wannan abu na da ban mamaki da kuma ban takaici“.

Lewis ya zargin ƙasashe masu hannu da shuni, da rashin cika alƙawuran da su ka ɗauka, na bada taimakon kudaden yaƙar wannan cuta.

A shekara banna an samu gibin dalla milion dari 5, na yawan kudadden da su ka ambata badawa.

Ya ce a ko wata a na kashe maggudan kuɗaɗe a yaƙin da ke wakana a kasar Irak, amma a game da yaƙi da cutar da zuwa yanzu,ta riga ta gama da mutane a ƙalla milion 25 ƙasashen na nuna halin ko in kulla.