1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron bitar kayan tarihi a Kano

June 26, 2009

An yi kyakkyawan fatan cewa wannan yunƙuri na UNESCO zai sa a ceto kayan tarihi na wasu ƙasashe da suke neman ɓacewa daga doron ƙasa baki ɗaya.

https://p.dw.com/p/Ic5z
Kasuwar Dawanau a jihar KanoHoto: DW

Hukumomin kula da tarihi da al´adu na ƙasashen Afirka Ta Yamma sun shirya wani taron bita a Kano a kwanakin baya don a zaɓo muhimman wuraren tarihi waɗanda za su kasance ƙarƙashin kulawar hukumar raya al´adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO.

Ƙasashen Afirka Ta Yamma dai su ne waɗanda ba su sami cikakken gata na kulawar kayayyakin tarihinsu a ƙarƙashin wannan hukuma ba musamman idan aka yi la´akari da ƙasashen Afirka Ta Arewa, waɗanda wasu daga cikinsu sun mallaki kayayyakin tarihi na dubban shekaru.

An nuna kyakkyawan fatan cewa wannan yunƙuri na UNESCO zai sa a ceto kayan tarihi na wasu ƙasashe da suke neman ɓacewa daga doron ƙasa baki ɗaya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Madobi