1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Charm El Cheick a game da Irak

May 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuMD

A Charm El Cheik, na ƙasar Masar, an buɗa taron ƙasa da ƙasa, a game da halin da ake ciki a Irak.

Wakilai daga ƙasashe fiye da 50 na dunia, sun fara gudanar da mahaurori da zumar lalubo mattakan tabbatar da zaman lahi a Irak.

Tun bayan ɓarkewar yaƙi a ƙasar, a shekara ta 2003, wannan shine taro mafi inganci a kan batun samar da zaman lahia a Irak, inji ministan harakokin wajen ƙasar Hoschiar Sebari.

Bayan batu zaman lahia, mahalarta wannan taro, za su shinfiɗa hanyoyin tada komaɗar tattalin arzikin ƙasar Irak, da yaƙi yayi wa raga-raga.

Sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleesa Rice, da Praministan ƙasar Iraki, Nuri Al Maliki, sun yi kira da babar murya, ga mahalarta taron, domin su himmantu wajen cimma burin da aka a sa gaba.

A ci gaba da taro, gobe idan Allah ya kai mu,ƙasashe masu maƙwabtaka da Irak, za su shirya ganawa ta mussamman, inda za su tatance gudumnmuwar bai ɗaya, da ta cencenta su bada, a yunƙurin kawo ƙarshen wannan rikici.