1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron duniya a kan canjin yanayi

November 16, 2009

Shugabannin ƙasashen Turai da kuma masu tasowa sun fara kai kawo domin ganin cewa sun yi angizo da zai kai ga samar da yarjejeniya kan ɗumamar yanayi a duniya.

https://p.dw.com/p/KYP8
Wakilan Ƙungiyar APECHoto: AP

Shugabannin ƙasashen Turai da kuma masu tasowa sun fara kai kawo domin ganin cewa sun yi angizo da zai kai ga samar da yarjejeniya kan ɗumamar yanayi a duniya, biyowa bayan jinkirtata da ƙasashen Asiya da Pacifik suka ce a yi a taron da birnin Copenhagen na Danmark zai ɗauki bakwaci makwani biyu masu zuwa.

Shugabar gwamnatin Jamus, wato Angela Merkel ta shiga sahun shugannin da suka tabbatar da cewa da su za a dama taron na Copenhagen saboda ruwa da tsakin da suke fatan yi domin ceto yarjejeniyar da a ke da niyar cimma. Wannan na me zama martani ga taron shugabannin ƙasashen Asiya da Pacifik da ya cimma matsaya game da jinkirta cimma sabuwar yarjejeniyar har bayan shekara ta 2009.

Bundeskanzlerin Angela Merkel Regierungserklärung Flash-Galerie
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture alliance/dpa

Suma ministocin da ke kula da harkokin muhalli na ƙasashe 40 na duniya sun fara gudanar da taron a birnin Copenhagen na kasar Danmark domin neman laluɓo hanyoyin tabbatar da nasarar taron kan sauyin yanayin da za a gudanar a watan gobe idan Allah ya kaimu. Suna masu danganta wannan yunƙuri da wani matakai na ƙarshe na neman samar da maslaha tsakanin ƙasashen da suka ci gaba da kuma ƙasashe matalauta game da bangaren da ya kamata ya samar da kuɗi shawo kan matsalar ɗumaman yanayi ga ƙasashe masu tasowa.

Firaministan ƙasar Danmark, ya tsara wata yarjrjrniyar siyasa wanda zai gabatar a taron na Copenhagen da ta taɓo muhimman batutuwa kamar rage yawan gurɓatecciyar iska, da kuma ƙayyade lokacin da za a cimma wata yarjejeniyar da ƙasashe daban daban za su yi na´am da ita a wani lokaci nan gaba.

Sai dai firaministan New Zealand, wato John Key ya ce da kamar wuya ƙasashen da suka yi ƙaurin suna wajen samar da gurɓatecciyar iska su bayar da kai.Ya kuma ƙara da cewa:

Regierungswechsel in Neuseeland John Key
P/M New Zealand John KeyHoto: AP

"A yanzu kowa ya lura da cewa babu wata yarjejeniyar da ƙasashe za su amince da ita a hukumance a taron sauyin yanayi da za a yi a birnin Copenhagen.Kuma babu wanda ya ke hasashen cewa saɓanin hakan zai faru."

sai dai kuma ƙasashen Afirka da ke zama kurar baya a fannin ci gaba da kuma ƙanana tsibirai game da wasu kasashen nahiyar turai sun jaddada bukatar da ke akwai na cimma kyakyawar yarjejeniya a taron na Copenhagen. Su dai waɗannan ƙasashe suna da ra´ayin cewa tilas ne kasashen da ke da ƙarfin tattalin arziki su amince da yarjejeniyar rage guɓatecciyar iskar kan nan da shekara ta 2020,kana su ware maƙudan kuɗaɗe domin tallafa wa kasashe matalauta su shawo kan matsalar ɗumamar yanayi da ke zama aman gashi a garesu.

sai dai kuma ƙasashen da suka ci gaban da ke ci gaba da fama da matsalar koma bayan tattalin arziki da kuma ƙaruwar marasa aikin yi suna ɗari-ɗarin yin wani alkawari.

Martin Kaiser da ke shugaban ƙungiyar kare muhalli ta Gren peace yayi tsokaci ya na mai cewa:

"A gani na bai kamata a ce Obama da ke da lambar yabo ta Nobel ya ƙi halartan wannan taron da ƙasashen duniya suka ɗora duk fatarsu a kai ba.Ita dai shugabar Gwmantain jamus za ta je kare matsayinta a Copenhagen game da ɗumam,ar yanayi. Abin da ya kamata Amirka da ke ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samar da gurɓatacce hayaƙi ta yi ke nan."

Ministan da ke kula da muhalli na kasar faransa Jean Louis Borleau ya bayyana cewa ƙasar Amirka, ita ce ke sahun farko na ƙasashen da ke kawo cikas wajen cimma yarjejeniyar da ta shafi sauyin yanayin.

Furuncin na Borleau ya biyo bayan wata takardar haɗin guywa da ke ɗauke da sa hannun shugaba Sarkozy da kuma takwaran aikinsa na Brazil, Louis Ignacio Lula Da sylva wadda ke da nufin sa ƙasashen da suke da ƙarfin tattalin arziki da su rage kashi 80 cikin ɗari na gurɓatecciyar iskar da masana´antu ke samarwa kan nan da shekara ta 2050.

Ya ce akwai bukatar cewa ƙasashen duniya su fara yin matsin lamba ga Amirka domin ta bayar da kai ga bukatar da ke akwai na cimma yarjejeniya da za ta bayar da damnar rage hayaƙin.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Ahmad Tijani Lawal