1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron duniya akan sabbin hanyoyin sadarwa a birnin Tunis

Mohammad Nasiru AwalNovember 17, 2005

Mahalarta taron kolin sun fi mayar da hankali ne akan samar da hanyoyin intanat ga kowa da kowa a duniya.

https://p.dw.com/p/BvUM
Utsumi, Annan da Ben Ali a zauren taron
Utsumi, Annan da Ben Ali a zauren taronHoto: AP

Masu iya magana dai kan ce da buba gara ba dadi. Gabanin a bude taron kolin na birnin Tunis Amirka ta fito karara ta ce ba zata yarda a tattauna game da ikon da take da shi na mallakar fasahar intanat ba, to amma yanzu ta sassauto game da sanarwar bayan taron da ake sa ran amincewa da ita a gobe juma´a. An tsara wannan sanarwar ce ta yadda kowa zai yi na´am da ita. Wato ma´aikatar cinikaiya ta Amirka zata ci-gaba da iko da hukumar ICANN wadda gudanar da aikin intanat din ya rataya a wuyanta. Jami´in dake kula da hukumar David Gross ya nuna gamsuwa da haka yana mai cewa.

“Mun gamsu da daftarin sanarwar bayan taron domin ya cike dukkan fatan da muka yi. Ya kuma nunar da muhimmincin fasahar sadarwa da kuma ta intanat tare da karfafa rawar da gwamnatin Amirka ke takawa wajen tabbatar da ingancin intanat din.”

Yanzu haka dai an amince a kafa wani kwamitin kasa da kasa wanda zai duba koke koke sauran kasashen duniya ciki har da na tarayyar Turai a game da ba su wani ´yanci na fadar albarkacin bakin su akan harkar ta intanat. A cikin shekara mai zuwa kwamitin zai fara taro to amma ba zai samu ikon zartas da wani hukunci ba.

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi maraba da wannan daidaito da aka cimma, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su budewa kowa da kowa hanyoyin amfani da intanat. Annan ya yi korafin cewa ana hanawa mutane da yawa a duniya yin amfani da sabuwar hanyar ta intanat. Annan ya ce samun hadaka ta intanat da komfuta da mallakar wayoyin salula ka iya zama gama gari a duk fadin duniya idan gwamnatoci suka nuna shirin yin haka. Annan ya tofa albarkacin bakin sa ga korafe korafen da ake yi musamman ma Amirka cewa MDD na son ta zama tamkar ´yar sandar duniya mai kula da harkar ta intanat.

“Ko kadan MDD ba ta da wani shirin zama wata ´yar sanda ko hukumar dake kula da intanat. MDD gamaiya ce ta kasa da kasa wadda ke tafiyar da aikin ta akan batutuwan da wadannan kasashe suka amince a kai. Burin mu dai shi ne mu kare hanyoyin intanat tare da ba wa kowa damar cin amfanin sa.”

To sai dai cimma burin na ba kashi 50 cikin 100 na al´umomin duniya baki daya samun hadaka ta intanat kafin shekara ta 2015 ba abu ne mai sauki ba. Hakazalika mene ne amfanin samar da na´urar komfuta ta tafi da gidanka ga wuraren da ba su da ma wata hadaka ta wayar tarfo. To duk haka dai babban sakataren kungiyar kamfanonin sadarwa na kasa da kasa Yoshio Utsumi ya ce shirya wannan taro kadai wata babbar nasara ce bisa wannan manufa.

“Wannan ba irin taron kolin nan ne da gwamnatoci kadai ke haduwa ba, a´a wannan taron ya hada wakilan kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyi na kasa da kasa da kuma kungiyoyin da kansu ya waye su kan san abin da duniya ke ciki don tattaunawa akan batutuwan da zasu amfani al´umomin duniya baki daya.”

A badi ne idan Allah Ya kaimu za´a gudanar da wani taro kan intanat don duba inda aka kwana a kan wannan batu.