1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron duniya kan barazanar nukiliya

Usman Shehu UsmanMarch 31, 2016

Batun nukiliyar kasar Koriya ta Arewa da tarzumar kungiyar IS sune za su mamaye jadawalin shugabannin kasarshen kimanin 50 da ke gudana a Amirka

https://p.dw.com/p/1IMXQ
Nuklear Gipfel Konferenz Atom
Hoto: AP

Taron wanda aka fara yau a birnin Washington, shi ne karo na hudu tun bayan kama mulkin shugaba Barack Obama na Amirka, wanda yace wai yana kokarin ganin bayan barazanar da makaman nukiliya ke kawo kan tsaro a duniya. Batun hana sarrafa nukiliya dai, shi ne babban abunda Obaman ya sa agaba tun hawansa kan mulki a shekara ta 2009. Ana saran shugabannin kasashen duniya kimanin 50 da wakilan kamfanoni za su tattauna, kan yadda za'a kiyaye rubbunan makaman nukilya da yanzu haka ke jibge a man'yan kasashen duniya. Akwai kuma batun samar da makashi da ake samu daga tashoshin nukiliya.