1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron duniya kan cutar ƙanjamau

August 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bumt

An buɗe babban taro na duniya karo na goma sha shida a birnin Toronto a kan yaƙi da cutar ƙanjamau. Taron ya buƙaci kawar da cutar daga doron ƙasa nan da shekara ta 2031, yayin da a hannu guda hamshakin attaijirin nan Bill Gates ya ci alwashin ƙarfafa yaƙi da cutar wadda ta hallaka mutane kimanin miliyan 25 a duniya. Mahalarta taron fiye da 20,000 daga ƙasashe daban daban sun yaba da samuwar maganin rage raɗaɗin ciwon a ƙasashen Afrika, sai dai sun ce akwai jan aiki a gaba wajen kawar da cutar daga nahiyar Afrika. Taron na kwanaki shida ya tattara masana kimiya tare da musayar raáyi da ƙarawa juna sani a kan yaƙi da cutar daga tushe. Bill Gates wanda ba da jimawa ba ya ƙaddamar da gidauniyar dala miliyan 500 don yaƙi da cutukan kanjamau, Tarin fuka da zazzabin cizon sauro ya yi imanin cewa mata na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen yaƙi da cutar, kana ya yi fatan zaá samo wasu magungunan waɗanda za su taimaka domin karya lagon cutar. Hukumar lafiya ta duniya ta yi ƙiyasin cewa fiye da rabin adadin mutane miliyan 39 dake ɗauke da ƙwayar cutar HIV mata ne.