1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ECOWAS da ECCAS akan fataucin bil adama

July 6, 2006
https://p.dw.com/p/BurS

Ministocin kasashen yammaci da tsakiyar Afirka sun bude wani taro na kwanaki 2 a Abuja,domin duba hanyoyin magance matsalar fataucin bil adama a kassahen Afirka.

Taron wanda kungiyar ECOWAS da kuma kungiyar tattalin arzikin kassaheb tsakiyar afrika ECCAS suka shirya zai bullo da wani sabon shiri na hadin gwiwa domin dakile wannan matsala tare da samarda yarjejeniya na hadin kai tsakaninsu.

Kungiyar UNICEF wadda itama ke halartar taron tace batun fataucin bil adama ya kai wani matsayi na ban tsoro a wadannan yankuna,inda tace a kashi 70 cikin dari na kasashen Yammaci da tsakiyar Afrika wannan babbar matsala ce data addabi jamaarsu.

UNICEF tace wannan matsala kuwa ta shafi yara kanana ne wadanda ake fataucin su zuwa kasashen turai da kasashen larabawa.