1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON E.U. A BRUSSEL YA CI TURA. SAI ME KUMA ?

Yahaya Ahmed.December 15, 2003
https://p.dw.com/p/Bvn5
Shirin da aka tsara na fadada kungiyar Hadin Kan Turai zuwa yankunan gabashin nahiyar, a cikin watan Mayun shekara ta 2004, na huskantar wata barazana, wadda idan ba a tashi tsaye ba, za ta iya janyo wargajewar manufofin kungiyar ma gaba daya. Taron da shugabannin kasashen kungiyar suka yi a karshen makon da ya gabata a birnin Brussels dai ya ci tura. Rashin jituwarsu a gun taron kuwa na nuna wa masu sa ido cewa, har ila yau mambobin kungiyar na nesa da cim hadin kai.

A halin yanzu dai, kasar Poland ce ake yi wa zargin gindaya wa ci gaban taron wani shinge, wanda ya hana sauran kasashen amincewa da kundin tsarin mulkin kungiyar. Tun ba ta shigo cikin kungiyar ba tukuna a zahiri, Poland ta fara nuna alamun kara aza mata kunama a kan gyambonta. To ina ma ga in ta zamo cikakkiyar mamba ta kungiyar a cikin watan Mayu mai zuwa k Kundin tsarin mulkin da aka zayyana dai, ba wata yarjejeniya ba ce, wadda a duk bayan `yan shekaru sun wuce, za a dinga sabuntata. A'a. A daura da haka, kundin zai zamo wani ginshiki ne wanda a shekaru da dama nan gaba, nahiyar Turai gaba daya za ta iya dogara kansa tamkar wani mizani na tsara makoman harkokinta da na al'ummanta.

Amma kawo yanzu, duk da muhimman tarukan da aka yi a Venice, a Italiya da Amsterdam a Holland, da dai ma sauran wasu wurare, kafin a yi taron baya-bayan nan a Brussels, ba a taka wata muhimmiyar rawar gani ba tukuna.

Ba za a iya dai zargin kasar Poland kadai da hana ruwa gudu a taron da shugabannin kungiyar suka yi ba. Jamus ma ba ta nuna sassaucin kaucewa, ko da ma kadan ne, daga nata bukatun ba. Jawaban da shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder ya yi gabannin taron ma, sun taimaka wajen angaza kasashen Poland da Spain, su ma su yi wa taron kunnen uwar shegu. Masharhanta dai sun kasa fahimtar barkewar rikici tsakanin Poland da Jamus kan batun samun murya fiye da daya, a tsarin ka da kuri'u a tarukan kungiyar. Da dai an tsaya kan shawarar da aka gabatar, da kasashen biyu ne ma za fi cin moriyar wannan tsarin.

A taron na Brussels dai, kasashen ba su nuna wata kyakyawar azama ta cim ma hadin kansu ba, kamar yadda manufofin kungiyar suka shimfida. Masu bin son zuci da kare maslahar kasashensu, su suka fi rinjayi wajen yi wa taron babakere.

Babu shakka, kundin tsarin mulkin na bukatar kwaskwarima da yawa. Amma ai da ya kamata , bayan taruka goma da aka yi kafin wannan taron na Brussels, a ce an cim ma wata madafa. To yanzu abin tambaya a nan dai shi ne, wai shin, ko da an sake kiran wani taron kuma, a kan me za a tattauna? Matsalolin da aka huskanci a birnin birnin Brussels a karashen mako dai, ba sa su bace hakan nan a cikin watanni 6 masu zuwa ba. To ga shi dai, a cikkin shekara mai zuwa ne al'umman Turai za su ka da kuri'u don zaben Majalisar nahiyar gaba daya. Amma za su yi hakan ne ba tare da sanin yadda makomar nahiyarsu za ta kasance ba.