1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron EU akan taaddanci8 a Brussels a mako mai zuwa

Zainab A MohammedAugust 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bu63
Kungiyar gamayyar turai EU zata gudanar da muhimmin taron kwararrun jamian tsaro cikin harkokin sufurin sama a mako mai zuwa a birnin brussels din kasar Belgium,domin tattauna shirin kai harin taaddanci da aka bankado a kasar Britania.Kasar Finland ,wadda ke rike da zagayen shugabancin kungiyar a yanzu,ta sanar dacewa ,taron zai gudana ne akarkashin jagorancinta da hukumar zartarwar EU.Wannan taron inji ofishin shugaban kasar ta Finland,zai tattauna daukan tsauraran matakan tsaro cikin harkokin sufurin sama,da kokarin kungiyar wajen yaki da ayyukan taaddanci.Adangane da hakane tuni ministan harkokin cikin gida na kasar Kari Rajamaki ya tuntubi takwarorinsa na Britania John Reid dana Jamus Wolfgang Shauble.A yanzu haka dai jamian yansanda daga wakilan kasashen dake kungiyar ta EU 25,na daukan tsauraran matakan tsaro tun bayan gano shirin kai harin taaddancin na Britania.