1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron EU da Iran game da makaman nukiliya

Hauwa Abubakar AjejeDecember 21, 2005

A yau ne kasar Iran da kungiyar taraiyar turai,suka koma teburin tattauna shirin nukiliya na Iran,wadda take nanata cewa tana da yancin sarrafa makamashinta,yayinda kasashen Amurka da turai suke ganin tana kokari ne na kera makaman nukiliya.

https://p.dw.com/p/Bu3A
Ahmedinejad na Iran
Ahmedinejad na IranHoto: dpa

Wani jamiin majalisar tsaro ta Iran ,Javad Vaidi,da suka fito cin abincin rana a yau daga taron,ya fadawa manema labarai cewa,taron,wata babbar dama ce ga bangarorin biyu su fahimci raayoyin juna.

Amma kuma jamian diplomasiya na kasashen yamma,tun farko sunyi gargadin cewa, samun nasarar shawo kan Iran tayi watsi da aiyukanta na nukiliya kadan ne.

Tattaunawar ta yau tsakanin jamian maaikatar harkokin waje daga kasashen Burtaniya,Faransa da Jamus da kuma tawagar Iran karkashin jagorancin Vaidi,itace ta farko tun bayan watsewar taron a watan Agusta,a lokacinda Iran ta koma harkokinta na sarrafa sinadarin uranium.

Sarrafa sinadarin na uranium dai shine mataki na farko da ake bi wajen kera makaman nukiliya ko samarda makamashi,duk da cewa kuma Iran din bata ci gaba daga nan ba,amma a yau din nan tace babu abinda zai hana ta ci gaba,inda tace tana da damar yin hakan karkashin yarjejeniyar hana yaduwar nukiliya ta kasa da kasa.

Iran din a halin yanzu tayi watsi da shawawar da kasar Rasha ta bata,na cewar ta gudanar da aiyukan sarrafa manta a cikin gida yayinda kasar Rashan zata taimaka mata sarrafa sinadarin na uranium a kasar ta Rasha,wanda yin hakan a cewarta zai kawadda batun kera makaman nukiliya na Iran daga idanun sauran kasashe.

Sai dai ministan harkokin wajen Iran,Manucher Mottaki,yace Iran zata iya bada tabbacin cewa ba zata sauya akalar aiyukan nata na nukiliya zuwa bukatu na soji ba.

Wannan matsayi da Iran ta dauka kuwa,ya zo ne a daidai lokacinda jamaa da dama suke kokawa da kalaman shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmedinajad game da kasar Israila,musamman na cewar a kawadda ita daga taswirar duniya baki daya.

Wani jamiin diplomasiya na Kungiyar Taraiyar Turai yace,ba abu ne mai sauki ba,janyo hankalin Iran ta dakatar da aiyukan inganta uranium tare kuma da neman ta baiwa kasashen duniya tabbacin cewa ba zata kera makamai ba.

Yace bangarorin biyu basu zauna tare sun tattauna ba tun watan Afrilu kuma a cewarsa gwamnatin Iran din ta canza tun daga wancan lokaci.

Wani jamiin Iran kuma yace,wannan tattaunawar ta share fage ne ga taro mai zuwa.

Shi kuma jakadan na Taraiyar turai cewa yayi,turawa a shirye suke su fuskanci gaskiya su kuma bambance tsakanin abinda ake bukata da kuma abinda abinda zai yiwu,musamman fayyace tsakanin anfani da uranium don inganta makamashi da kuma kera makamai.

Rashin samun nasarar wannan tattaunawar a wannan karo dai,zai ingiza turawa da kuma Amurka,wacce take goyon bayan Kungiyar ta Turai,amma bata cikin tattunawar,kai kasar Iran gaban komitin sulhu na majalisar dinkin duniya.

Ita dai Amurkan tana musun cewa,ba zaa taba yarda da Iran cewa ba kera makaman nukiliya take shirin yi ba,ita kuma Iran tana son akalla a bata damar yin bincike akan yadda zata inganta makamashinta.

Kasar Rasha kuma wadda take da ikon darewa kujerar naki a majalisar,kuma a yanzu take gina tashar nukiliya ta farko a Iran,tace babu alamar cewa Iran din tana kokarin kera makaman atom,kuma akwai yiwuwar cewa Rashan zata kawo cikas game da batun kaiwa Iran gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.