1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron farko na ministocin harkokin wajen kasashe 26 na kungiyar NATO.

Mohammad Nasiru AwalApril 2, 2004
https://p.dw.com/p/Bvkt
Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar NATO na kallon faretin soji a gaban hedkwatar kungiyar a birnin Brussels
Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar NATO na kallon faretin soji a gaban hedkwatar kungiyar a birnin BrusselsHoto: AP

Bayan da a hukumance aka yi bikin shigar da kasashe 7 sabbin membobin kungiyar tsaro ta NATO a birnin Washington a ranar litinin da ta wuce, a yau juma´a an gudanar da wani faretin soji a hedkwatar kungiyar dake birnin Brussels. Sabbin kasashen kuwa su ne Bulgaria, Estonia, Latvia, Lithuania, Romania, Slovakia da kuma Slovenia.

Sakatare-janar na kungiyar NATO Jaap de Hoop Scheffer shine yayi jawabin yin lale marhabin da sabbabbin membobin kungiyar daga yankin gabashi da tsakiyar nahiyar Turai a gun wannan taro, wanda shine irinsa na farko da ministocin harkokin wajen kasashe 26 suke yi. Mista Scheffer ya ce shigar da wadannan kasashen cikin kungiyar ta kawo karshen rarrabuwar nahiyar Turai. Yanzu abin da aka sa gaba shine a hada kai don yakar ta´addanci sannan ya kara da cewa:

"Mun yi murna kuma mun yi farin ciki da haka. Kofar kungiyar NATO a bude ta ke ga kowace kasa da ke da sha´awar kare manufofin mu."

Kasashen da ake shirye-shiryen daukan su cikin kungiyar nan gaba su ne na yankin Balkan kamar Kuratiya da Macedoniya da kuma Albaniya.

A na ta bangaren ministar harkokin wajen kasar Estonia Kristina Ojuland ta bayyana wannan rana a matsayin wata rana ta yin alfahari da farin ciki, wadda ba zata taba mantawa da ita ba. Shi kuma ministan harkokin wajen Slowakia Eduard Kukan cewa yayi sabbin membobin zasu bi dokokin wannan kungiya sau da kafa don karfafa ta.

To sai dai ba dukkan ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ta NATO suka hallara a wannan biki ba. Alal misali ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer, to amma ana sa ran zai halarzi taron nan gaba, inda ministocin zasu tattauna game da halin da ake ciki a Iraqi da kuma Afghanistan.

Sakataren harkokin wajen Amirka Colin Powell na matsawa kungiyar ta NATO lamba da ta gaggauta karbar ragamar shugabancin membobin ta 18, wadanda a halin yanzu suka tura dakarunsu kasar Iraqi don radin kansu, amma ba karkashin tutar kungiyar ba. Kasar Poland alal misali tana son ta mikawa kungiyar NATO yankin da ke hannunta a Iraqi. Yayin da ita kuma sabuwar gwamnatin kasar Spain ke shirin janye dakarunta gaba daya daga Iraqi. Shi dai sakataren harkokin wajen na Amirka na sa ran cewa kafin ranar daya ga wata yuli, za´a zartas da wani sabon kuduri a kwamitin sulhu, wanda zai ba MDD damar taka muhimmiyar rawa a Iraqi. Idan aka samu haka to kasashen Spain da Faransa ka iya girke dakarunsu a Iraqi a karkashin lemar MDD.

In baya ga kasar Slovania dukkan sabbin membobin sun goyi bayan yakin kasar Iraqi ba tare da gindaya wani sharadi ba. Saboda haka Amirka ke sa ran cewa zata fadada angizonta a cikin NATO bayan fadada ta da aka yin. Shi ma kwamandan rundunar NATO janar Harald Kujat na da ra´ayin cewa nan ba da dadewa ba kungiyar zata mika kai ga bukatun Amirka. Kuma za´a amince da hakan a hukumance a gun taron kolin kungiyar, wanda zai gudana a birnin Istanbul a karshen watan yuni idan Allah Ya kaimu.