1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G8 a Jamus.

June 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuJk

Gobe idan Allah ya kai mu, ƙasashe 8 mafi ƙarfin tattalin arziki a dunia, ke buɗe zaman taron su, a birnin Heiligendamm na ƙasar Jamus.

Tunni tawagogin sun fara sauka a wannan birni, da a halin yanzu ya kasance a kanun labarun dunia.

Za a gudanar da wannan taro a cikin tsatsauran matakan tsaro, domin an kewaye birnin na Heiligendamm,da wani dogon shingen ƙarfe, mai tsawan kilomita 12, wanda kuma jamai´an tsaro dubu 16 su ka yi wa zobe.

Yan sa´o´i ƙalilan kamin fara wannan taro, masharahanta sun hango cewar, babu shaka,wannan haɗuwa za ta kasace tamkar wani ƙasaittacen membari, inda za a cacar baki, tsakanin shugaba Bush na Amurika, da takwaran sa na Russie, Vladmir Putine, a game da batun garkuwar kakkabo makamai masu lizzami, da Amurika ta ƙudurci kafawa, a wasu ƙasashen turai, da na Asia.

Kazalika, za a fuskanci matsananciyar ɓaraka, a game da batun rage ɗumamar yanayi.

Gwamantin Jamus ta tabatar da cewa, ta shirya tsap ,domin ganin wannan taro ya wakana lami lahia.