1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G8 da G20 a Kanada

June 25, 2010

An fara taron shugabannin ƙasashen duniya a Kanada, inda za su tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/O2kl
Shugabannin ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arzikiHoto: AP

Shugabannin ƙasashen duniya sun fara hallara a Toronto ƙasar Kanada. Ƙasashe takwas masu ƙarfin masana'atu a duniya wato G8, da kuma a gefe guda ƙasashe 20 mafiya ƙarfin tattalin arziki na G20. duk a yau suke haramar taron kwanana uku a ƙasar ta Kanada. Taron G8 dai zai maida hanakaline kan cigaba da kuma batutuwan da suka shafi tsaro. Inda ranar Lahdi da yamma ƙasashen G20 su hallara don tattauna batun sauyin da suke so duniya tabi wajen tattalin arziki. Ganin cewa shugabannin duniya mafiya faɗa ajine ke hakllaratan taron, an baza dubban yan sanda don tsaro, inda har ajiya suka kama wata mota maƙare da ababen facewa ciki hara da ma haɗin gida kusa da inda shugannin zasu hallara. kuma an kama wassu mutanen biyu da suke shirya kai harin bam a ƙolin.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana buƙatar shiga a dama da ita da kuma ƙulla ƙawance ne a wajen taron ƙungiyar ƙasashe takwas da suka ci gaba a fannin tattalin arziƙi, ba wai ta miƙa kokon barar agaji ba daga gare su. Jakadan Najeriya a ƙasar Kanada Iyowuese Hagher, ya shaidawa manema labarai hakan, Hagher yace duk da cewa Najeriya ta yi na'am da irin matsaloli da ƙalubalen na cin hanci da kuma rashin samarwa 'yan ƙasar abubuwan more rayuwa, to amma a yanzu ba za'a ce da irin matsalolin ne kawai za'a rinƙa kallon ƙasar ba. Bayan isar sa ƙasar Kanada, da yammacin Alhamis shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, zai gana da wakilan kamfanonin ƙasashen da ke cikin ƙungiyar G20, kana kuma shugaban na Najeriya zai halarci taron ƙungiyar ƙasashe takwas dake da ƙarfin tattalin arziƙi ta G8, gabannin ya komo gida Nijeriya. 

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas