1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

010309 EU Sondergipfel Abschluss

Mohammad AwalMarch 2, 2009

Shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai sun yi watsi da shawarar kafa asusun ko ta kwana don tallafawa ƙasashe mambobin ƙungiyar da ke tsakiya da kuma gabashin Turai waɗanda arzikinsu ya fuskanci koma baya.

https://p.dw.com/p/H42J
Shugabannin EUHoto: picture-alliance/ dpa

A taron ƙoli na gaggawar da suka kammala jiya a Brussels, shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai sun yi watsi da shawarar kafa asusun ko ta kwana don tallafawa ƙasashe mambobin ƙungiyar da ke tsakiya da kuma gabashin Turai waɗanda arzikinsu ya fuskanci koma baya. To amma sun tashi daga taron suna masu alƙawarin mutunta dokokin da suka shafi kasuwancin bai ɗaya, yayin da matsalar tattalin arziki ke ƙara taɓarɓarewa.

An dai kira wannan taro ne a wani mataki na shawo kan matsalar tattalin arziki da ke ƙara yin ƙamari a duniya. Batuwan da suka fi addabar sabbin ƙasashen da suka shiga ƙungiyar ta Tarayyara Turai dai; sun haɗa da batun basussuka da kuma wahalhalun dake tattare da biyan basussukan. Har ila yau kuma da yadda bankuna ke ƙara rugujewa.

Donald Tusk zu Raketenschildplänen der USA
Firaministan Poland Donald TuskHoto: AP

Fira ministan ƙasar Poland Donald Tusk ya yi magana a madanin ƙasashe da dama na Tarayyar Turan, in da ya bayyana tsoron da wasu ƙasashen suke da shi na cewar, masu ƙarfi daga cikinsu na neman danne marasa ƙarfi.

Ya ce muna fatan cewa ƙasashen Turai za su yi watsi da ɗabi'ar da suke da ita yanzu na kowa tasa ta fisshe shi, muna fata mu zamanto tsintsiya maɗaurinki ɗaya wajen warware matsalolinmu na tattalin arziki, ta yadda za a samar da wani tsarin ciniki na bai ɗaya da kowacce ƙasa za ta ci moriyarsa ba cuta ba cutarwa, kamar dai yadda yake a yarjejeniyar gammayyar ƙasashen Turai.

'Yan kwanaki kaɗan dai kafin wannan taro shugaba Sarkozy na Faransa ya bayyana wa 'yan jaridar Jamus canja tsarinsa na ceto kamfanonin motocin ƙasar ta Faransa wadda ake ta kace na ce akansa.

Finanzkrise in Frankreich: Präsident Sarkozy will Arbeitsplätze retten
Shugaban Faransa Nikolas SarkozyHoto: AP

Ya ce Faransa ta ƙuduri aniyar canja tsarinta na ceto masa'antun ƙasar yadda zai yi dai dai da ƙa'idojin kasuwancin bai ɗaya da Tarayyar Turai ta amince da shi, alƙalla wannan ma wani daddaɗan labari ne a gare mu''

To sai dai duk da haka akwai wasu ƙanan ƙasashen ƙungiyar ta Tarayyar Turan, da suke a tsakiyar gabashin Turai waɗanda bulaliyar tattalin arzikin ta basu ɗan karen kashi. Misali ƙasar Hungary wadda bashi yai mata katutu, kuma bankunansu suke fuskantar durƙushewa. Wannan ne ma dalilin da ya sa ƙasar ta Hungary ta yi kira ga Tarayyar Turan da ta kafa asusun ko ta kwana, na dala biliyan dari biyu da talatin don tallafawa ƙasashe mambobin ƙungiyar dake tsakiya da kuma gabashin Turai, waɗanda arzikinsu ya fuskanci koma baya. Batun da ƙasar Jamus ta nuna dawa da shi; ga dai abin da Angela Merkel ta ce.

"Misalin abin da ke faruwa a ƙasar Hangary ya nuna cewa akwai ƙasashen da suke buƙatar taimako na musamman daga gare mu, amma fa ina ganin ba dukkanin ƙasashen da ke tsakiyar gabashin Turai ne ke cikin irin wannan hali ba''.

Merkel vor der American Academy in Berlin
Angela Merkel shugabar gwamnatin JamusHoto: AP

Amma duk da wannan hali da ake ciki, Angela Merkel ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wajen tunawa gwamanatocin ƙasashen Turan da ake bi bashi cewa, kada fa su mance da biyan bashin da ke kansu.

"Ta ce yana da kyau a ɓangare ɗaya a yi batun yadda za a fita daga ƙangin tattalin arzikin da ake ciki, amma kuma a daya bangaren ya zama wajibi a rika tunanin hanyoyin da za a bi wajen rage basussukan da ake bin kasashe, domin a rage ci da gumin rayuwar al'ummar da za su ci gaba da rayuwa a bayanmu''.

To sai dai maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa yanzu domin ceto tattalin arzikin, ya yi yawan da ake ganin cewa wannan doka ta ceto tattalin arzkin bai ɗaya a nahiyar Turai, aiwatar da ita a aikace fa abin da kamar wuya.

Abba Bashir