1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron haɗin ƙasa a somalia

August 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuET

A birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia, ana ci gaba da taron haɗin kann ƙasa, wanda aka fara ranar 15 ga watan juli da ya gabata.

Wakilin mussamman na Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Dunia, a ƙasar Somalia Fransois Fall, ya halarci zaron a yau, inda ya gabatar da jawabin Bankin Moon.

Fall ya tabatar da cewar Majalisar Ɗinkin Dunia na bada cikkaken goyan baya, da mahimmanci, ga wannan taro, wanda ta ɗorawa yaunin lalubo hanyoyin fidda somalia daga tashe-tashen hankulla da ta ke fuskanta.

Bugu da ƙari, ya alƙawarta gummuwar ƙungiyar ta ƙasashen dunia domin wanzuwar ƙudurorin da wannan taro zai tsaida.

Saidai Fransois Fall, ya bayyana rashin gamsuwa, a game da rashin halartar wakilan dakarun kotunan Islama, wanda su ka haramta taron, su ka kuma ɗauki alwashin tarwatsa shi, ta ko wace hanya.