1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hukumar IAEA a birnin Vienna

September 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuBF

Gobe ne idan Allah ya kai mu, a birnin Vienna, na ƙasar Austriyya, hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ke gudanar da zamna taro koli.

Wannan taro zai haɗa ƙasashe 144 membobin hukumar, zai kuma tantana a game da halin da ake ciki a rikicin nuklear ƙasashen Korea ta Arewa da Iran.

Taron zai wakana, a daidai lokacin da shugaban hukumar IAEA, Mohamed Albaradei , da mataimakin sa, ke shan suka, daga ƙasashen turai da Amurika, a game da abinda su ka kira, sako- sako da su ke nunawa, wajen warware rikicin nuklear ƙasar Iran.

A ɗaya wajen, wannan taro, zai maida hankali a kann makomar makashi a dunia, nan da shekaru 20 masu zuwa.

A yayin da wakilin Amurika ke huruci kamin fara wannan taro, ya nunar da cewa, ranar 21 ga watan da mu ke ciki, ƙasashe 6 masu shiga tsakanin rikicin nuklear Iran, za su shirya zaman taro a birnin Washington, domin tunanin sabin hanyoyin ƙargamawa Iran takunkumi.

Ministan harakokin wajen France, Bernard Kouchner a lokacin da ya ke fira da yan jarida a yau lahadi, ya hurta cewar, bisa dukkan alamu, sai an yi anfani da ƙarfin soja kamin ciwo kann Iranta yi watsi da shirin ta na mallakar makaman nuklea.