1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hukumar kare yaduwar nukiliya

February 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9b

Hukumar kare yaduwar nukiliya ta duniya tana ci gaba da tattaunawa a yau kan batun kaiwa Iran gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

A halin yanzu dai kasashen Rasha da China sun amince da wani kudirin Kungiyar Taraiyar Turai na sanarda komitin sulhu halin da Iran take ciki,muddin dai an baiwa Iran din waadin zuwa watan maris domin ta bada hadin kanta ga masu bincike na Majalisar, kafin daukar mataki a kanta,wanda ya hada da yiwuwar kafa takunkumi..

A jiya alhamis ne hukumar ta fara taronta domin yanke shawara akan shirin nukiliya na Iran.

Kasashen Turai da Amurka suna fatar samun kuriar amincewa da kaiwa Iran din gaban komitin sulhu.