1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Islama

YAHAYA AHMEDNovember 15, 2005

Taron, wanda kasar Autriya ke karbar bakwancinsa, ya sami halartar manyan shugabannin kasashen musulmi kamarsu Afghanistan da Iraqi da kuma Iran.

https://p.dw.com/p/BvUS
Vienna
ViennaHoto: dpa

„Addinin islama a jam’in al’ummai na duniya“, da wannan jigon ne gwamnatin kasar Austriya, ta kwatanta taron wanda ta shirya take kuma karbar bakwancinsa. A cikin jawabinsa na bude taron jiya abirnin Vienna, shugaban kasar Austriyan, Heinz Fischer, ya bayyana fatar cewa, ta wannan hanyar ta tuntubar juna dai, za a iya shimfida wata gada, wadda za ta taimaka wajen inganta fahimtar juna tsakanin al’ummomi daban-daban na duniya. Kamar yadda ya bayyanar:-

„Idan aka yi la’akari da hauhawar tsamari da rikice-rikice a duniya a halin yanzu, inda wasu kungiyoyi da gungun masu tsatsaurar ra’ayin islama ke ta ikirarin haddasa wasu daga cikinsu, to babu shakka irin wannan tattaunawar na da muhimmanci kwarai a wannan lokaci fiye da yadda ake zato.“

A ganin shugaban na Austriya dai, Turai za ta iya kambama kanta a huskar kare hakkin dan Adam, da bai wa jama’a damar bayyana ra’ayoyinsu da tafiyad da harkokin addininsu, ba tare da an muzguna musu ba. kasar Austriya dai, inji shugaba Fischer na da tsohuwar al’ada ta girmama addinai, musamman ma dai addinin islama:-

„“Ana iya ganin haka ne a irin girmamawar da addinnai kamar addinin islama ke samu a nan Turai, inda kuma wannan kasar ta Austriya ce daya daga cikin farkon kasashen Turai da suka amince da addinin islaman a hukumance tun cikin shekarar 1912, tafarkin da take bi kuma har ya zuwa yanzu.“

A cikin manyan bakin da suka sami damar yin jawabi jiya har da tsohon shugaban kasar Iran, Muhammad Khatami, wanda ya gabatar da wata makala kan „jam’in al’ummai da halin rayuwa na wannan zamanin“. Khatami ya yi kira ne ga duk al’ummomi da su girmama addinai da al’adun da suka bambanta da nasu. Ta haka ne za a iya samun zama cikin kwanciyar hankali da lumana a duinya baki daya. A zamanin da muke cikin nan dai, inji tsohon shugaban na Iran, yi wa wata kasa ko wani bangare saniyar ware, ba abu ne da zai janyo fa’ida ba. Kuma yiwuwar hakan ma na da wuya, saboda a ko’ina wani rikici ya barke, za a sami angizonsa a duk duniya baki daya. Sabili da haka ne yake ganin ba daidai ba ne, ko wane ne ma ya yi amfani da labarn tarihi wajen ta da kurar rikici ko kuma yaki.

Ministan harkokin wajen Austriya, Ursula Plassnik, ta ce kasarta za ta kara ba da kaimi wajen shirya irin wannan taron na tuntuba da addinin islama, idan ta karbi jagorancin kungiyar Hadin Kan Turai tun daga farkon watan Janairu:-

„Wannan taron na „Addinin islama a jam’in al’ummai na duniya, wato gudummuwarmu ke nan kafin ma mu karbi jagorancin kungiyar Hadin Kan Turai na farkon watanni 6 na shekara ta 2006. Turai dai, nahiya ce mai son zaman lafiya, wadda kuma burin da ta sanya a gaba ne tabbatad da aminci, da gafarta wa juna da kuma fahimta tsakanin al’ummomin duniya.“

Duk da wadannan kalamun masu dadin ji dai, a gun taron an girke jami’an tsaro ne a ko’ina, da shirin ko ta kwana. Ana binciken kowa da ya kusanci zauren taron, har da ma `yan yawon shakatawa.