1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron J 8 a Rasha

July 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bur1

Yara matasa yan da su ka hito daga ƙasashe 8, mafi ƙarfin tattalin arziki a dunia, wato G8 sun buɗa wani mahimin taro a birnin Pouchkine na ƙasar Rasha.

Wannan haɗuwar ƙananan yara manyan gobe, na matsayin share fage, ga taro ƙoli da zai haɗa shugabanin G8, a ƙasar Rasha tsakanin15 zuwa 17 ga watan da mu ke ciki.

Wannan shine taro irin sa na farko, a tarihin, G8, wanda matasa yan shekaru 13 zuwa 17 a dunia, za su masanyar ra´ayoyi, su kuma hurta albarakacin bakin su, ga shawarwarin da shugabani masu faɗa a aji, a dunia za su tsaida wa.

K0 wace daga ƙasashen 8 na G 8, ta aika wakilai 8, a taron na matasa, wanda Hukumar International Morgan Stanley, tare da haɗin gwiwar UNICEF su ka zaɓa, ta hanyar gasar Video.