1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron jami´an diplomasiya a Nairobi kan halin da ake ciki a Somalia

January 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuVV
´Yan diplomasiyar kasashen Yamma da takwarorinsu na Afirka sun gana a birnin Nairobi inda suka tattauna akan samar da jami´an kiyaye zaman lafiya da kuma taimako ga kasar Somalia. Wata kungiyar kasa da kasa dake tuntubar juna akan halin da ake ciki a Somalia ta gudanar da taro da shugaban Somalia Abdullah Yusuf a daidai lokacin da sojojin Somalia da na Ethiopia suka yiwa mayakan kotunan Islama kawanya a kusa da kan iyakar Kenya. Kungiyar dai ta hada da Amirka da kasashen KTT. A kuma halin da ake ciki wani faifaye dake dauke da muryar mataimakin shugaban Al-Qaida, Ayman al-Zawahiri yayi kira da ´yan Islaman na Somalia da su shiga yin wani yakin sunkuru shigen na Iraqi.