1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron jam'iyar Christian Social Union a Kreuth-Jamus

Rabi GwanduJanuary 8, 2007
https://p.dw.com/p/Btwl
Edmond Stoiber shugaban jam'iyar CSU
Edmond Stoiber shugaban jam'iyar CSUHoto: dpa

Jami’yar CSU ta jahar Bavaria, wadda take mulkin jahar dake yammacin Jamus tun kusan shekaru 50 da suka wuce, jami’iyar ce ta kawance da babban jami’iyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel. Edmond Stoiber wanda ya dade yana rike da shugabancin jami’iyar, a yanzu hakan yana tsakiyar wata tabargaza ta lekan asiri a cikin jamai’iyar tasa. A lokutan zaman taron su a wurin shakatawa dake Wilbad Kreuth, shugabannin jami’iyar CSU sau da yawa sun cimma nasara wajen kaucewa dubarorin juyin mulki a jami’iyar, amma a wannan karon zasu fi mayar da hankali su ne wajen kawo doka da oda a harkokin cikin gida. Shugaba Stoiber yana fama da barazanar rikici da ta dabaibaye wani babban jami’in sa wanda ake tuhuma da laifin leken asirin wasu daga cikin jamiy’an jamiyar.Daya daga cikin manyan jami’an CSU Gabriele Pauli, a yau litinin ta sake nanata kira ga Stoiber da ya amsa laifi ya aje mukamin sa na shugabancin jami’yar. Inda take cewa:

O-TON: Babu wata shakka a game da irin gudumawar da ya baiwa jahar Bavaria, kuma dole ne a cigaba da tunawa da shi a game da hakan, amma akwai mutane da dama wadanda suke da imanin cewar lokaci yayi da ya kamata yayi murabus, sabili da suna fatan ganin ya cimma karshen aikin sa na siyasa cikin mutunci.“

Uwar-gida Paula itace babbar shugaba wadda aka sani da bayyana ra’ayin ta a game da harkokin da suka shafi jmai’iyar, bayan da aka gano cewar daya daga cikin makarraban Stoiber yana neman tattara wasu rahotannin siri a game da ita. Ance ma har sai da ya kai ga bin didigin rayuwan ta na soyyaya da wasu halayen ta na shaye shaye.

O-TON PAULA:

Ya ya Stoiber ya hada da…“

Paula tayi ikirarin cewar tana da goyon bayan wasu manyan jami’ai masu bukatan ganin Stoiber ya yi murabus. Wannan rikicin ya kan iya zama wani tabo a rayuwar siyasan Edmond Stoiber wanda yayi shekaru 13 yana jan ragamar mulkin jahar Bavaria tare da samun goyan baya daga dukkan jami’an jam’iyar ta CSU. Amma abin mamaki yanzu shine wani sakamakon bincike da aka buga dazu dazun nan da ke nuna cewa kashi 62 na al’uman Bavaria suna adawa da burin Stoiber na tsayawa takara a zaben yankin da za’a gudanar cikin sahekara mai zuwa, a yayin da ake cigaba da yayata jita-jita akan shirin gudanar da zaben cikin gida domin tsayar da sabon shugaban jam’iya, wanda ake karfaffa zaton cewar ba zai karbu ba daga manyan jami’ai ba. Markus Söder shi ne sakatare janar na CSU, ga kuma abinda yake cewa:

O-TON: Watau cecekucen da ya samo tushin sa daga bakin uwar-gida Paula baya da wani nufin haifar da alhairi a harkokin jam’iyar CSU ba, illa dai wata hanya ce ta shafa wa Stoiber kashin kaji. Kuma tun fiye da shekaru 50 da suka wuce ne makarraban CSU suka tsayar da shugaban jam’iyar, kuma kawo yanzu ta cimma nasarori daban daban karkashin wannan mulkin wanda aka kafa domin cimma kyakyawar makoma.“

Da wannan bayyanin ne ake ganin jam’iyan CSU a shirye suke su kare mutuncin Edmond Stoiber lokacin