1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Kara Wa Juna Ilimi Akan 'yan Gudun Hijira a Berlin

June 22, 2004

A yau aka kammala wani taron kara wa juna ilimi akan 'yan gudun hijira a nahiyar Turai, wanda hukumar 'yan gudun hijira ta MDD da Mujami'ar evanjelikan ta Jamus suka dauki nauyin gudanar da shi a Berlin

https://p.dw.com/p/Bvim
Manema mafakar siyasa a filin jiragen saman Frankfurt
Manema mafakar siyasa a filin jiragen saman FrankfurtHoto: AP

A dai halin da ake ciki yanzu matsalar manema mafakar siyasa, matsala ce ta bai daya tsakanin illahirin kasashen Turai kuma a saboda haka ya zama wajibi akan sabbin kasashen da aka karba a inuwar Kungiyar Tarayyar Turai watan mayun da ya wuce su yi biyayya ga dokokin da kungiyar ta tanadar bisa manufa. A dai halin da ake ciki yanzu yawan masu gabatar da takardun neman mafakar siyasa a sabbin kasashen tuni ya zarce na tsaffin kasashen kungiyar ta tarayyar Turai idan an kwantanta da yawan al’ummominsu. Ta la’akari da haka ya zama wajibi a yi bitar lamarin domin yin raba daidai tsakanin illahirin bangarorin da lamarin ya shafa. An ji wannan bayanin ne daga Claudia Roth, wakiliyar gwamnatin Jamus akan hakkin dan-Adam a lokacin da take jawabi a zauren taron kara wa juna ilimin a Berlin. Jim kadan kafin karbar kasashen na gabacin Turai aka cimma daidaituwa aka wasu ka’idojin da aka tanadar bai daya, musamman a game da ‚yan gudun hijirar da kan kaurace daga kasashensu ba a bisa dalilai na siyasa ba. Stephan Berglund, wakilin hukumar ‚yan gudun hijira ta MDD a Jamus, ya yaba da irin ci gaban da aka samu a game da wani muhimmin bangare na kare makomar ‚yan gudun hijira a nan kasar, inda nan gaba zata rika karbar ‚yan gudun hijirar dake kauracewa daga kasashensu bisa dalilai na yaki ko rikicin addini ko na kabilanci da makamantansu. Shi ma wakilin mujami’ar Evanjelikan ta Jamus Stephan Reimers yayi batu a game da wani muhimmin canjin dake ba da kwarin guiwa akan manufa. To sai dai kuma wakiliyar gwamnati akan hakkin dan-Adam tayi korafi a game da cewar ba a yi batun ba da damar ci gaba da zama a Jamus ga manema mafakar siyasar a sabuwar dokar kaka-gidan da aka cimma daidaituwa kanta tsakanin gwamnati da #yan hamayya a ‚yan kwanakin baya-bayan nan ba. Bisa ga ra’ayinta wajibi ne ‚yan gudun hijirar da suka yi shekara da shekaru suna tafiyar da al’amuran rayuwarsu a Jamus su samu kafar zama na dindindin a kasar. Claudia Roth, ‚yar jam’iyyar the Greens ta ce wani abin damuwa kuma shi ne ganin yadda kasashen KTT ke kokarin danka wa kasashe da ba na kungiyar ba alhakin kula da makomar ‚yan gudun hijira, inda a yanzu haka ake batu a game da sallamar maneman mafakar siyasar zuwa kasashen dake wajen iyakokin kungiyar tarayyar Turai domin bitar takardunsu. Wannan wata manufa ce da za a iya kwatanta da matakin neman dirke manema mafakar siyasa a ketare. To sai dai kuma akasarin kasashen kungiyar na adawa da wannan ra’ayi. Wasu daruruwan ‚yan zanga-zanga suka yi cincirindo a kusa da zauren taron domin bayyana adawarsu da matakan da mahukunta na KTT ke dauka wajen korar manema mafakar siyasa. Wasu manema mafakar siyasa kimanin 50 daga kasashen Togo da Kamaru sun shiga yajin kin cin abinci domin janyo hankalin jama’a zuwa ga mawuyacin hali na siyasa da ake ciki a kasashensu, suna kuma masu neman da a ba su cikakkiyar dama ta ci gaba da zamansu a nan Jamus. Wata kungiyar kare hakkin ‚yan gudun hijira ta Jamus tayi bayani a game da mawuyacin halin da ake ciki a kasar Togo inda mahukunta ba sa shayin azabtar da fursinoni da kisan gilla akan abokan adawa, amma duk da haka yawan ‚yan kasar dake da ikon samun mafakar siyasa a kasashen Turai bai taka kara ya karya ba.