1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasa na Democrat a Denver

Zainab MohammedAugust 26, 2008

A yau ne Hillary clinton zata yi jawabi a taron ƙasa na jami'iyyar Demokrat

https://p.dw.com/p/F5Lg
Hillary Clinton a taron DenverHoto: AP

A cigaba da taron kasa na jami'iyyar Demokrat a Amurka,a yau ne tsohuwar 'yar takara kuma 'Yar majalisar Dottijan kasara zatayi jawabin,dake da nufin janyo magoya bayanta domin su marawa Abokin takararta Barack Obama baya, ayunkurinsa na shiga fadar gwamnati ta white house.

Ɗan takarar kujerar shugabanci a karkashin tutar jami'iyyar Demokrat Obama dai na fatan ganin cewar an cimma ɗunke saɓanin daya shiga tsakaninsu,alokacin zaɓen fidda gwani,wanda hakan ne zai bashi goyxon bayan 'yan gani kasheni dake goyon bayan Clinton,wadanda har yanzu ke adawa da nasararsa da kuma zaɓan Joe Biden, a matsayin mataimakinsa.

wannan na daya daga cikin irin tallace tallacen yakin neman zaɓe na jami'iyyar Republican a Amurkan...

"Ina alfahari da goyon bayan Hilary Clinton ta jami'iyyar Demokrat,amma a karon farko yanzu na koma goyon bayan ɗan takarar jami'iyyar Repulikan John McCain"

Sai dai ayar tambaya anan itace,shin mata nawa kamnar yadda wannan tallan ke nunarwa suka koma ɓangaren McCain? yanzu jite jiten dake yaɗuwa tsakanin jami'iyyar ta Demokrat shine cewar,kowane daya daga cikin magoya bayan Hillary Clinton biyar,zasu zaɓi John McCain a zaben ranar 4 ga watan Nuwamba.

A taron kasa na Demokrat din dake gudana a Denver dai akwai wakilai da dubban magoya bayan Hillary....

"Sunana Linette Garber,shekaru na 55 da haihuwa,kuma ina daya daga cikin wakilan Hillary".

Linette Garber dai Wakiliya cedaga Kalifonia,wadda ke sanye da rigar T-Shirt dake dauke da hoton Senato Hillary gaba da baya,wadda kuma ke zama daya daga cikin wakilanta a lokacin zaɓen fidda gwani.

Taron na Denver dai na fatan ganin cewar an samu daman haɗe kan magoya bayan uwargidan tsohon shugagaban Amurkan,domin marawa Barack Obama baya domin ya cimma nasarar shiga fadar gwamnati ta white house.Kamar yadda Joanna Casio daga Geogia tayi nuni dashi...

"Na kaɗa kuri'ata wa Hillary,saboda a wannan lokacin ina ganin babu wanda ya cancanci wannan matsayi face ita,amma yanzu Obama shine ya samu nasara ,kuma ya zamanto wajibi mu mara masa baya"

To sai dai kuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni dacewar mafi yawa daga cikin magoya bayan Hilary sun gwammace zaɓen McCain a maimakon Obama.Acewar ɗaya daga cikin 'yan gani kashenin dake goyon bayan Hillary wannan jite-jite ne kawai na kafofin yada labaru...

"A ganina kafofin yada labaru na hakan ne da nufin haifar da ɓaraka ,amma sanin kowa ne mutane kalilan ne ke da wannan ra'ayi,domin babu yadda magoya bayan Hillary zasu jefawa McCain kuri'arsu."

Itama Linette Garber,na ganin cewa mutane dayawa suna bin zuciyarsu ne kwai amma ba abunda yafi dacewa kasa ba...

"Mutane,na bin son zuciyarsu akan batutuwa kamar wannan,maimakon ayi la'akari da abinda ya cancanci kasa,don haka dole mu zabi Ɗan jami'iyyar Demokrat zuwa fadar gwamnti ta White House"