1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashen duniya kan halin da ake ciki a Zirin Gaza

September 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bukt

Wani taron kasashen duniya a birnin Stockholm ya tara kudi kusan dala miliyan dubu daya a matsayin agaji ga kasar Lebanon. Yanzu haka dai wadanda suka shirya taron na fatan cewa kasashe da kuma kungiyoyi zasu dauki irin wannan mataki a wani taron da za´a yi yau juma´a don samar da kudaden taimakon jin kai ga Zirin Gaza. Kimanin kasashe 50 da kungiyoyi da suka halarci gun taron kann kasar Lebanon sun yi alkawarin samar da dala miliyan 940 a matsayin taimakon gaggawa da nufin sake gina Lebanon. Mahalarta taron zasu ci-gaba da zama a birnin na Stockholm don tattaunawa akan wahalhalun da Falasdinawa ke ciki, wanda masu shirya taron suka ce ya tabarbare yayin da hankalin duniya ya karkata ga yakin kwanaki 34 da aka gwabza tsakanin Isra´ila da Hisbollah. Babban jami´n dake kula da ayyukan jin kai na MDD Jan Egeland ya bayyana halin da ake ciki a Gaza da cewa wani bam ne da ke shirin fashewa a kowane lokaci.