1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashen kudancin Amurka

December 10, 2006
https://p.dw.com/p/BuYZ

Shugabannin kasashen kudancin Amurka ,a karo na farko sun tattauna matakan daukan tsauraran matakai na hadin kann siyasa ,a karshen taronsu na yini biyu.Shugaban kasar Bolivia Evo Marales,wanda ke zama mai masaukin bakin wannan taro,yace manufofoin alummomin kasashen kudancin Amurka adangane da kafa kungiya kamar ta tarayyar turai ,zai iya cimma buri nanda da shekaru biyar masu gabatowa.Shugabanni da wakilan kasashe 12 da suka halarcin taron na yini biyu,sun cimma yarjejeniyar kafa headquatarsu ta wucin gadi a birnin Rio de Janeiro,wadda zata dauki alhakin shirya kungiya guda,da yiwuwar kafa majalisar gudarnawa ta kasashesn kudancin Amurkan.