1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kokarin rage talauci a duniya

September 22, 2010

Merkel ta ce taimakon kai - da - kai ne kawai zai warware matsalar talauci a kasashe masu tasowa

https://p.dw.com/p/PIt6
Hoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda ke cikin jerin shugabannin kasashen duniyar da ke halartar taron bitar manufar bunkasa - ta karni wadda aka fi sani da Millenium Development Goals ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na Amirka, ta bayyana cewar, bai kamata kasashe su dogara akan alkawura - na har illa - ma - sha - Allahu ba, maimakon haka - a cewar ta kamata ya yi kasashe su bayar da fifiko ga bunkasa kasashen su da kansu, da kuma tabbatar da cewar suna yin kyakkyawan amfani da irin albarkatun da Allah ya hore musu. Merkel ta furta kalaman nan ne a lokacin jawabin da ta yiwa kimanin shugabannin kasashen duniya 140, wadanda suka hallara domin nazarin shirin bunkasa kasashe ta hanyar inganta ilimi da rage talauci da kuma cututtukan da ke addabar jama'a - a karkashin shirin nan da Majalisar Dinkin Duniya ta yiwa take da "MDG", wanda kuma kasashen duniya suka yi na'am da shi shekaru 10 da suka gabata.

Shirin dai ya fuskanci cikas saboda kariyar tattalin arzikin da kasashen duniya daban daban suka fada ciki a shekaru ukkun da suka gabata. A yanzun nan da ake batu kuma kiyasi ya nuna cewar akwai bukatar samar da zunzurutun kudi dalar Amirka akalla miliyan dubu 120 domin cimma manufar rage talauci - akalla da rabi nan da shekaru biyar masu zuwa.

A wani ci gaba kuma Majaisar Dinkin Duniya ta yi nasarar samun alkawuran kudi na dalar Amirka miliyan dubu 40 domin sashen kula da lafiya ga kasashen duniya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu