1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli na kungiyar ASEN a birnin Kwalalalampur

December 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvGq

Yau ne a birnin Kwalalampur na kasar Malaisia a ka buda taron kungiyar Asean, da ta hada kasashe 11 na kudu maso gabacin Asia.

Babban burin da mahalarta taron su ka sa gaba, shine na kara karfafa mu´amilar cinikaya tsakanion su.

Su na masu bukatar cimma matsayin kasashen kungiyar gammaya Turai, da su ka yi nasara dage shingen cinikaya, da na biyan kudaden harajin Kustom a tsakanin su.

Kazalika, za su hiddo da wani tasri na hadin gwiwa, domin fuskantar annobar massara kaji da a yanzu, ta jallaka mutane 70 ,a wannan yanki tare da jawo assara mai yawa.

A hannu daya, kasashen zasu masanyar ra´ayoyi a game da matakan tsaro.

Kasashe China da Japon da Korea ta kudu suma za su halarci wannna taro, sannan ranar laraba a na sa ran karabar wasu sabin Membobi, da su jka hada da, Austarliya, India da New Zeland, ko kuma Nouvelle Zellande.