1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin kasashen kudu maso gabashin Asiya

Ibrahim SaniNovember 20, 2007
https://p.dw.com/p/CJUI

An buɗe taron ƙungiyyar haɗin kan ƙasashen kudu da gabashin yankin Asiya, a ƙasar Singapore. Taron zai mayar da hankaline kan batu na kare hakkin Bil´adama da kuma hulɗar kasuwanci, a tsakanin mambobin ƙasashen.To amma duk da haka , batun ƙasar Burma shi ya fi ɗaukar hankalin mahalarta taron. Mambobin ƙungiyyar ta kudu da gabashin yankin na Asiya Goma ne su ka janye amincewarsu na gayyartar wakilin Majalisar ɗinkin duniya na musanman a ƙasar ta Burma,izuwa wannan taron ƙoli. Hakan dai ya biyo bayan ƙin amincewar gayyar Ibrahim Gambarin ne daga Gwamnatin ta Burma. Bukatar zuwan Mr Gambari taron ƙolin nada nasaba ne da yiwa taron ƙolin cikakken bayanin halin da ake cikine a ƙasar ta Burma.