1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin Kungiyar Tarayyar Turai

December 15, 2005

A yau shuagabannin KTT ke fara taron kolinsu a Brussels

https://p.dw.com/p/Bu3M
Frank-Walter Steinmeier
Frank-Walter SteinmeierHoto: AP

An saurara daga bakin ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier yana mai bayanin cewar a yanzun bayan da aka kasa cimma nasarar gabatar da daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai wajbi ne a mayar da hankali wajen samun wani ci gaban da kungiyar zata yi alfahari da shi. Wannan maganar musamman ta shafi cimma daidaituwa ne akan kasafin kudinta da ake neman gabatarwa daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2013, lamarin da aka sha fama da sabani kansa a karkashin shugabancin kasar Luxemburg ga KTT a watanni shida na farkon wannan shekara. Steinmeier ya ce:

Idan har muka sake nuna gazawa a karo na biyu dangane da maganar kasafin kudin to kuwa ba shakka hakan ka iya zama wata mummunar alama ga jama’a. Bugu da kari kuma sabbin kasashen kungiyar sune zasu fi jin radadin wannan gazawa.

Ita dai Birtaniya fatanta shi ne ta ga an kayyade yawan kudaden taimakon da ake ba wa kananan kasashe na kungiyar domin cike kasafin kudinsu, lamarin da zai fi shafar sabbin wakilai a kungiyar, amma a daya bangaren kasar ta Birtaniya ta ki ta amince da a rage yawan alfarmar da ake mata game da kudadenta na gudummawa ga asusun Kungiyar ta tarayyar Turai. Steinmeier ya ce wajibi ne kowace kasa ta ba da gudummawa gwargwadon karfinta. A nasa bangaren wakilin ‚yan Christian Union a majalisar dokoki Andreas Schockenhoff ya fito fili ne yana kalubalantar shugabancin watanni shida da Birtaniya tayi ga kungiyar, inda ya ce babu wani sakamako na a zo a gani da aka samu daga shugabancin nata, inda aka bata lokaci ana fama da maganganu na fatar baki kawai. Ita dai Jamus, wadda kawo yanzu ta fi kowace kasa ba da gudummawa mai tsoka ga baitul-malin KTT, a yanzun al’amuran sun kai mata iya wuya kuma ba ta sha’awar yin kari akan abin da ta saba bayarwa. Sai dai wasu daga cikin wakilan ‚yan hamayya na ganin hakan ragon azanci ne da kuma rashin hangen nesa, saboda Jamus, a matsayinta na kasar da ta dogara kacokam akan fitar da kayayyakinta zuwa ketare domin samun kadaden shiga, tana samun amfani daga kungiyar ta tarayyar Turai. A yau ne dai shuagabannin kasashen kungiyar suka gabatar da taronsu na yini biyu a Brussels, inda a baya ga maganar kasafin kudin za kuma a mayar da hankali ga kalaman da suka fito daga bakin shugaban kasar Iran Mahmud Amhmadinajad a baya-bayan nan na la’antar Isra’ila, wanda kuma yake kwatanta kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa a nahiyar Turai tamkar almara. Jamus tayi Allah waddai da wadannan bayanai tana kuma fatan gabatar da maganar domin yanke wani kuduri kanta a zauren taron kolin.